Daga: Bello Hamisu ida
Littafin Sabo da Maza shi ne littafin
da ya lashe gasar Aliyu Mohammed Hausa Book Prize 2018 wanda Aliyu Mohammed
Library, Gusau Institute Kaduna ke shiryawa duk shekara. Za ku iya sauke PDF
din littafin Sabo da Maza ta hanyar latsa nan Download a wayoyin hannunku.
Abinda masana suka ce game da littafin;
Professor Malumfashi Ibrahim:
Jigon Labarin 'Sabo da Maza' shi ne hali da tsaro ke ciki a Kasar Nijeriya musamman ma kan 'yan tayar da kayar baya. Salo da Jigon Labarin ya yi ma'ana kuma zai rike mai karatu, zai rike mai karatu ba tare da sanin me zai faru gaba ba. Tsarin Jera jarumai ya yi kyau, ba a cakuda su ba, ta inda mun san jarumin mu, duk wanda ya zo bayansa mataimakin jarumin ne.
Sayidda Rahma Abdulmajid:
Marubucin Littafin 'Sabo da Maza' na daban ne da salonsa ya sace tunanina tsaf. ban zaci akwai sauran irin wa ɗannan marubuta ba da suka yi saura, ashe akwai.
Malama Halima Ahmad Matazu:
Labarin SABO DA MAZA ya yi ma`ana kuma ya ƙayatar ta hanyar yin nuni cikin nishaɗi. Zubin labarin ya taɓo batutuwa da dama da suka shafi ta'addanci da rayuwar soyayya da fyade da kissan gila da auratayya da al`adu da imani da aƙidu da ɗabi`u da tunani musamman na Arewacin al'ummar Nijeriya tun a zamanin mulkin soja, a haka har aka taho zamani da rayuwar mulkin siyasa na wannan lokacin, saƙonninsa sun isar da ma`anarsa wacce ta kasa ɓoyuwa, cikin tsari da zubin rubuce-rubucen Hausa na zamani.
Abu na gaba shi ne salon labartawar labari. SABO DA MAZA ya zo da zubin (third-person omniscient narrator); ma`ana makaranci yana ko`ina, yana sanin halayen taurari da abin da suke ciki.
SOMIN TABIN LABARIN
Labarin ‘SABO DA MAZA’ labari ne na
wani Soja mai suna Bashir Bello wanda ya ɓace a dajin Sambisa a ranar farko da sojoji suka
fara shiga wannan rikitaccen dajin. Rokar su Bashir, ita ce rokar da ta fara
kutsawa cikin dajin. Sune kuma sojoji na farko da suka fara fito-na-fito da
tsagerun da suka ɓoye cikin dajin. Labarin
ya bayyana yadda sojoji suka sha wahala sosai kafin su kutsa cikin rikitaccen
dajin, wanda tsagerun suka zagaye da ababen fashewa. Sojojin sun rasa
rayukansu, suka rinƙa kashe junansu ba tare da sun sani ba. Labarin ya
bayyana yadda ƙabilu daban-daban suke rayuwa a cikin rikitaccen
dajin Sambisa.
Labarin ya yi walƙiyar rayuwar bariki watau yadda ‘ya’yan
sojoji suke rayuwa a cikin bariki, da kuma yadda talakawa, matsakaita da masu
kuɗi
suke kallon rayuwar waɗannan yara. Labarin ya fassara yadda muhalli ke
juya al’umma, ta yadda al’ummar
take kallon muhalli. Bashir tauraron labarin ya ɗanɗana rayuwar kunci, ya rayu cikin bariki inda Barasa
ta zama kamar mahaifiyarsa wace ke bashi shawarar yadda zai gudanar da
rayuwarsa ta yau da kullum. Haka kuma ya ɗanɗana rayuwar gidan yari inda yayi mu’amala
da mutane daban-daban, haɗa da ɓarayi, ‘yan fashi, matsafa, mayaudara,
mazanbata da kuma masu satar mutane don ƙarɓar kuɗin fansa.
Duk da yake a lokacin bai rutsa shekara
ashirin ba, amma hankalinsa ya wuce na manya saboda cuɗanya da yayi da mutane daban-daban. A
zamansa na gidan yari, ya fahimci cewa a ƙasar Najeriya mai laifi shi ne sakakkiyar akuya,
yayin da masu gaskiya suke ɗaure. Haka kuma, masu tsaron ƙasa watau irinsu, yansanda, kostam,
imagirashin, da su kansu sojojin, mafi yawansu duk tsaffin mashaya ne irinsa,
ake wa wankan tsarki a sakaya su da kakin aikin. Wannan shima ya ƙara taimaka sosai wajen taɓarɓarewar tsaro a cikin ƙasa, ta yadda masu kaki suke aikata
laifuffuka irinsu fashi da makami, sata da kashe junansu.
Labarin ya yi walƙiya ya bayyana matsalolin da ƙasarmu ta shiga sanadiyar siyasa,
matsalar ƙauraye,’yan
bangar siyasa, tsagerun Nija-delta, mayaƙan boko haram, faɗan makiyaya da manoma, tashe-tashen
hankullan Kano, Kaduna da Jos, faɗan ƙabilanci da sauransu. Labarin
ya hakaito yadda rashin aiki ya yi tsanani a tsakanin matasa, wanda ya sanya su
shiga mumunan ɗabi’u kamar; shaye-shaye, barace-barace, ƙauranci, sace-sace, fashi da makami,
kisan, a ƙasar
Najeriya.
Labarin ya zo da salon jan hankalin
makaranci ta yadda zai karance ɗinbin labarin ba tare da ya ankara ba, haka kuma
anyi amfani da salon iya jan zaren labari da yin amfani da taurari daban-daban.
Anyi amfani da kalmomin da suka dace da kowane muhalli na labarin, da salon
magana, da karin magana, da iya sarrafa harshe; an nutsar da karin magana a ƙalla guda dubu ɗaya a cikin labarin waɗanda suka dace da muhallin da aka yi
amfani da su a cikin labarin. Marubucin labarin ya yi ƙoƙari sosai wajen jan zaren labarin inda ya raba
labarin zuwa kasha-kashi, haka kuma an tamke (ɗaure) kowane babi da ɗan’uwansa ta yadda labarin ba zai gundurar
ba.
0 Comments