GABATARWA
An rubuta wannan littafi mai suna ‘Hausa
Firamare 1’ don ya yi daidai da manhajar koyarwar Firamare 1 (Primary
Curriculum), zubin littafin ya yi daidai da sabuwar Manhajar Hausa wadda
Hukumar Bincike da Haɓaka Ilimi ta Nijeriya (NERDC) ta sabunta a shekarar 2018. An sauya sunan
littafin daga ‘Sabuwar Hanyar Koyon Karatu da Rubutu a Hausa’ zuwa
‘Hausa Firamare 1’ domin samu sauki wajen furucin sunan littafin.
Ga Darussan
da ke cikin littafi na Ɗaya:
JIGO |
KARAMIN JIGO |
DARUSSA |
HARSHE |
A1. Sauraro Da Magana |
A1.1 Sunayen Abubuwa A1.2 Kalmomin Aiki A1.3 Taɗi A1.4 Ƙidaya |
A2. Karatu |
A2.1 Karatu Kafin Fara Babbaƙu A2.2 Karatun Babbaƙu |
|
A3. Rubutu |
A3.1 Rubutu Kafin Fara Babbaƙu A3.2 Rubuta Babbaƙu |
|
ADABI |
B1. Wasan Kwaikwayo |
|
B2. Waƙoƙi |
B2.1 Waƙoƙin Yara B2.2 Waƙoƙin Baka Da Rubutattun Waƙoƙi |
|
B3. Zube |
B3.1 Tatsuniya |
|
AL’ADA |
C1. Ɗabi’u Da Al’ada |
C1.1 Ladabi Da Biyayya C1.2 Gaisuwa C1.3 Tsafta C1.4 Ranakun Mako |
C2. Ginshiƙin Ginin Al’umma |
C2.1 Kulawa Da Iyali |
|
C3. Kayayyakin Al’adu |
|
A latsa nan Hausa Primary 1 don sauke PDF ɗin littafin, Littafin kyauta ne ga
Malaman Makaranta masu koyar da harshen Hausa Firamare 1. Idan an samu tangarda
wajen saukewa a sake jarabawa.
3 Comments
sannunku da ƙoƙari
ReplyDeleteSannunka da kokari mun samu litattafan da zamu koyar da yaranmu a firamare
ReplyDeletemuna maku barka da kokari, lallai wannan littafi ya yi amfani sosai ga yara yan Primary 1 zuwa 6, na yi amfani da shi kuma na ji dadinsa sosai. Allah ya saka wa Marubucin littafin Bello Hamisu Ida da alkairi ya kara basira.
ReplyDelete