Ɗalibai su ba da bayanin zane da kwalliya
daban-daban, su tantance ire-iren zane da salon kwalliya da tufafi, su bayar da
bayanin zane da kwalli da tufafi. A yi amfani da hotuna da jadawali zane da
kayan kwalliya da sarƙa da
murjani da awarwaro da malafa da hula wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai
su amsa tambayoyi.
Zane
Zane ko Tsagar ado, ko kuma shasshawa, akan yi ta ne
domin kawa da karin kwalliya domin fuska ta yi kyau ko kuma wani bangare na
jiki wanda zai iya daukan ido. Bisa al’adar Bahaushe, a kan yi zane a fuska ko
wasu ɓangarori na jiki don bambance
zuri’ar wannan gida da wancan gida. Amma wasu lokutan akan yi zane a jiki domin
neman magani bisa wata cuta da ta kama wanda aka yi wa zanen, misali, idan
ciwon kai ya addabi jariri ko babba a kan yi masa fashin goshi don a samu sauƙin ciwon kan.
Ga misalan irin zane da ake yi don bambance zuri’a:
1. Bille
2. Gassgawa
3. Kwale
4. ‘Yar baki
5. Kalangu
6. Kwalliya
7. Kitso
8. Kwalli
Kwalliya
Bayan wannan zane da ake, a kan yi wasu kalolin
zanen don kwalliyar jiki, ga misalan wasu daga cikin zane da ake yi a jiki don
kwalliya:
1. Kitso (Wannan mata ke yinsa don yin kwalliya bisa
kai ta hanyar yin zanen kitso da gashin kai)
2. Lalle wato ƙunshi
3. Aski (Wannan maza ke yinsa don yin kwalliya bisa kai
ta h
4. anyar cire gashin dake saman kai)
Kayan Kwalliya
Bayan zane na jiki da kuma kwalliyar jiki, akwai
kayan kwalli da ake amfani da su don ƙara ƙawata jiki ya samu gamshashiyar
kwalliyar da ake buƙata, Bahaushe
yak an yi amfani da kayan kwalliya.
Ga misalin wasu daga cikin kayan
kwalliyar Bahaushe:
1. Sarƙa
2. Ɗan kunne
3. Murjani
4. Tsakiya
5. Jigida
6. Awarwaro
7. Takalmi
8. Agogo
9. Munduwa
10.
Malafa
11.
Hula
Dukan waɗannan ana sanya su a jiki ne domin ƙawata jiki da gamsasshiyar kwalliya, akwai waɗanda maza ke sanyawa kamar ‘hula’ akwai kuma wanɗanda mata ke sanyawa kamar ‘sarƙa’, akwai kuma waɗanda maza da mata na sanyawa kamar ‘agogo’.
0 Comments