Ɗalibai sub a da bayanin ire-iren bukukuwan sallah. A yi
amfani da hotuna da littafi da rediyo da talabijin da bidiyo da kaset da faifan
CD wajen koyar da ɗalibai,
daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.
Ma’anar Bukukuwa da Wasanni
Biki taro
ne da ake yi a domin taya juna, ko farin ciki lokacin da aka samu ƙaruwar haihuwa ko za a ɗaura aure. A kan yi nishaɗi da kiɗe-kiɗe da
raye-raye wajen sannan ci, a sha domin nuna farin ciki. Ana yin ire-iren wannan
biki a ranakun ƙaramar
Sallah da babbar Sallah da kuma maulidi don nuna farin cikin zagayowar ranakun.
Misalan
bukukuwan Hausawa su ne kamar haka:
1. Bikin
Sallah Ƙarama
2. Bikin
Sallah Babba
3. Bikin
Maulidi
4. Bikin Aure
5. Bikin Suna
Bayanin Bikin Sallah Ƙarama Da Babba
Ana wadannan bukukuwan ne
bayan kammala azumin watan Ramadan da kuma ƙarshen shekarar musulumci. Shi hawan salla biki ne da
sarakuna ke gabatarwa a ranakun ƙaramar sallah da babbar sallah, akan fara bikin hawan sallah ne daga filin idi. Sarki
yana yin ƙasa da kyalliya ya hau dokinsa tare da hakimansa da digantansa da sauran masu riƙe da muƙaman sarautar gargajiya.
Kowane ɗaya daga
cikinsu zai hau dawakai da tawagarsa cikin kwalliya daga su har dawakan nasu,
suna tafiya jama’a kuma na kewaye da su suna
kallo suna miƙa gaisuwa. A ranar farko a kan tashi daga filin idi zuwa gidan sarki.
Idan aka je gidan sarki, sai a jira sarki ya zo ya sauka tukuna, sannan duk
sauran hakimansa ɗaya-bayan-ɗaya su je su yi gaisuwa. Bayan an kammala kuma sai sarki ya yi jawabi ga
jama’ar ƙasarsa baki ɗaya sannan a
sallami kowa ya watse.
Washegari kuma
sai a ci gaba, wanda wannan ya kan bambanta daga masarauta zuwa wata
masarautar. Kowace masarauta akwai takamaiman wani guri da sarki ke zuwa a
wannan rana, su kuma jama’a su fito gefen hanya suna miƙa gaisuwa ga
sarki, fadawa kuma suna karɓa.
Bayanin Bikin
Maulidi
Maulidi wani biki ne da Musulmai ke yi duk shekara don tunawa da haihuwar Manzo Allah Annabi Muhammad (saw). Ana yin Maulidi ne a duk
12 ga watan Rabi'
al-awwal ta shekarar Hijira. Musulmi a fadin duniya ne ke
bikin maulidin kuma suna fitowa domin bayyana farin cikinsu.
Ana karatun Al’kur’ani da kuma jawabai na tarihi da fadakarwa ne a
guraren taron maulidi; hade da shagulgulan walima da wakokin yabo ga Manzon
Allah (s.a.w) don bayyana farin ciki.
0 Comments