Talla

C2.3 Bikin Suna: Marubuci Bello Hamisu Ida

 

Bikin Suna

Ɗalibai su san ma’anar bikin suna su san yadda ake gudanar da bikin suna, su san muhimmancin bikin suna. A yi amfani da talabijin da rediyo da bidiyo da litattafai da kaset da katuttuka. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

Ma’anar Bikin

Biki shagali ne da ake nuna farin ciki wajen aure ko suna ko naɗin sarauta ko salla ko al’adun gargajiya ko ma al’adun da zamani ya zo da su.

Yadda Ake Gudanar Da Bikin Suna

Bikin suna biki ne da ake gudanarwa a ranar da aka yi kwana bakwai da haihuwa, a ranar ne ake raɗa suna sannan ayi shagali. Akan fito da abinci jama’ar da suka taru su ci, su kuma maroƙa da makaɗa suna kaɗe-kaɗensu, ana bas u abin masarufi.

Bayan kuma an gama wannan, sai mata su haɗu yawanci daga farkon rana har zuwa maraice, suna ‘yan kaɗe-kaɗe, da waƙe-waƙensu na mata, suna guɗa da sauransu. Sannan kuma sukan zo da kyaututtuka a matsayin gudunmawa ga ita mai haihuwar.



Idan kuma haihuwar fari ce, to, akan samu mata su taru a gidan iyayen mai jego; wato gidan mata kenan, su haɗo nasu abubuwan. Bayan sun tattara abubuwan da suka tara, sai kuma su ɗauko shi da maraice zuwa gidan da aka yi haihuwa, su zo su rarraba ga iyaye, da sauran dangin miji. Wannan rabo shi ake kira tsaraba. A wannan zamani, a kan je wa mai haihuwa taron suna don taya ta murna da kuma bata ƙaututuka na gudumuwar bikin su.

Muhimmancin Bikin Suna

Bikin suna yana da muhimmanci, ga kaɗan daga cikin muhimmancinsa:

1.     Yana ƙara danƙon zumunci tsakanin ‘yan’uwa da abokan arziƙi inda ake taruwa don taya juna murnar samun ƙaruwa.

2.     Akan samu nishaɗi da annashuwa da farin ciki wajen bikin suna.

3.   Yana ƙara bayyana matsayin zumunci a cikin al’umma, har ma wasu na ganin in ba aje taya su murnar suna ba, to an rage masu matsayi.

 Aikin Aji

1.     Yi bayanin bikin suna?

2.     Yi bayanin yadda ake gudanar da bikin suna?

3.     Yi bayanin muhimmancin bikin suna guda biyar?



Post a Comment

0 Comments