Talla

C2.2 Sana’oi: Marubuci Bello Hamisu Ida

 

Sana’oi

          Ɗalibai su ba da bayanin sana’o’in Hausawa sub a da bayanin muhimmancin sana’o’i. A yi amfani da jadawalin sunayen sana’o’I da hotuna da jarida da komfuta da faifan CD da litattafai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

Ma’anar Sana’a

Sana’a hanya ce ta sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa ɗan’adam waɗanda suke kewaye da muhallinsa. Mutane suna yin sana’a ne, domin samun abin masarufi don gudanar da harkokin rayuwa na yau da kullum. Akwai Sana’oin Hausawa da dama, ga misalin wasu daga cikinsu:

1.     Noma

2.     Ƙira

3.     Kiwo

4.     Jima

5.     Tiƙo

6.     Ɗinki

7.     Da sauransu

Bayanin Yadda Ake Aiwatar Da Sana’ar Noma

Noma shi ne gyara ƙasa da shuka iri, da fitar da amfaninta gona waɗanda suka ƙunshi kayan abinci da sauran abubuwan buƙata na masarufi. Noma tsohuwar sana’a ce a ƙasar Hausa, wadda aka dogara da ita domin samun abinci. A kan fara noma bayan faɗuwar damuna. A irin wannan lokaci, tun kafin lokacin manoma kan shirya, ta hanyar kai taki da sharar gona da aiwatar da dukkan abubuwan da ya kamata.

 


 

Nauo’in Noma

Akwai noma iri biyu a ƙasar Hausa, su ne kamar haka:

1.            Noman Damina.

2.            Noman Rani.

Yadda Ake Gudanar Da Sana’ar Noma


Tun kafin saukar damina, manoma sukan fara shirye-shirye ta hanyar sharar gona da kai taki da sassabe da cire tushiya. Da zarar ruwan sama ya sauka, sai a yi shuka ana tona ƙasa ana zuba iri, ana binnewa. Bayan shuka ta yi kamar mako biyu, sai a yi noman farko, Idan kuma ta ƙara tasawa, sai a yi maimai. Daga ƙarshe sai a yi sassarya. Idan kuma shuka ta nuna sai a girbe, a yanke sannan a yi dammai a kai gida don amfani.

Muhimmancin Sana’o’i

1.     Dogaro da kai

2.     Samar da abinci

3.     Samar da ariziƙi

4.     Tsare mutunci

5.     Haɓɓaka damina

Aikin Aji

1.     Ba da bayanin sana’o’I guda biyu da Hausawa ke yi?

2.     Ba da bayanin muhimmancin sana’o’i guda biyar da aka sani?

Post a Comment

0 Comments