Tsarin sarautun Hausawa
Ɗalibai su ba da bayanin sarautun Ƙasar Hausa
da yadda ake naɗin sarauta a Ƙasar Hausa sannan su tantance sunayen sarautu da ayyukansu a Ƙasar Hausa.
A yi amfani da rawani da alkyabba da algaita da hoton tambari da hoton doki
wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.
Ma’anar Sarauta
Sarauta
wata hanya ce ta shugabantar jama’a ta hanyar samun iko da damar mulkar su da ɗora su bisa turba a ƙarƙashin jagorancin Sarki wanda
ke riƙe da masarauta. sarauta wani
tsari ne na tafiyar da harkokin mutane na yau da kullum.
Al’ummar
Hausawa suna da tsarin sarautunsu na gargajiya don tafiyar da harkokin mulkin
jama’a cikin sauƙi. Wannan tsari na sarautu da
Hausawa suke amfani da shi wajen wakilci sun haɗa da: Sarki da Hakimi da Dagaci da Mai
unguwa da kuma sauran jama’ar gari.
Yadda Ake Naɗin Sarauta A Ƙasar Hausa
Naɗin sarauta wata hanyace ta
tabbatarwa da wanda aka zaɓa aka ɗora shi a kan mulki, aka kuma yarda da ba shi wata
sarautar gargajiya a Ƙasar Hausa. A rana ta bikin naɗin sarauta, a kan yi biki. Za
a gayyato manya da ƙananan masu riƙe da sarautun gargajiya, da
kuma sauran jama’a zuwa wajen wannan biki don taya wanda za a naɗa murna.
Idan
za a naɗa Sarkin a wata Masarauta, a kan yi ƙasaitaccen biki, a shirya hawa da sauran shagulgula
masu ƙayatarwa, a shirya sukuwar dawakai da folo
da makamantansu.
Ana yin
girke-girke, a gayyato mawaƙa da makaɗa da maroƙa. Ana tanadar manyan riguna, na alfarma kamar alkyabba da takalmi da
kuma rawani, wanda za ayi naɗi. A cikin fada ne
za a zaunar da wanda za a naɗa a saka masa waɗannan riguna, a naɗa masa rawani. Da zarar an gama naɗin, sai a yi ta kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ana buga tambura. Sai kuma da yammacin wannan rana da
aka yi naɗin sarauta, mutane irin su Hakimai da
Dagatai da masu Unguwanni, da kuma ‘Ya’yan Sarki, su yi ta zuwa suna kai wa
sabon Sarki gaisuwa, tare da taya shi murna.
A wajen naɗa sarki, ‘yan majalisar sarki ne suke zaɓar mutane uku, daga cikin masu neman sarautar, sannan
su miƙa wa gwamna, ya zaɓi ɗaya sai kuma a
tabbatar da shi. Sarki ne yake zaɓar wanda yake so, domin ya naɗa shi hakimi. Dagaci kuwa, jama’ar gari ne suke zaɓa daga cikin masu takara. Wanda ya sami jama’a mafi
yawa, shi ne ake naɗawa. Sai wanda ya gada ne yake yin
sarautar Dagaci. Mai-unguwa dagaci ne yake naɗa shi, ko ya gada ko bai gada ba.
Tantance Sunayen Sarautu
Da Ayyukansu A Ƙasar Hausa
Ga yadda
tsarin sarautun Hausawa ya ke da ayyukkansu:
Sarki: Shi ne shugaba kuma mai ba
da umarni kowa yana ƙarƙashin ikonsa.
Hakimi: Shi ne mai kula da gunduma,
wanda ƙauyukan Dagatai suke ƙarƙashinsa.
Dagaci: Shi ne mai kula da ƙauye guda ɗaya, daga cikin ƙauyukan da ke ƙarƙashin kulawar Hakimi.
Mai unguwa: Shi ne mai kula da unguwa
guda ɗaya daga cikin unguwannin da
ke ƙarƙashin garin dagaci cikin ƙauye guda ɗaya.
Sauran jama’a: Su ne al’ummar gari waɗanda ake mulka.
Aikin Aji
1.
Yi cikakken bayani
a kan sarautun Ƙasar Hausa?
2.
Bayyana yadda ake
naɗin sarauta a Ƙasar Hausa?
Kawo sunayen sarautu da ayyukansu a Ƙasar Hausa?
0 Comments