Ɗalibai su lissafa hanyoyin sufuri iri-iri, su iya kawo amfanin hanyoyin sufuri. Ayi amfani da hoton doki, hoton jaki, littafi, hotuna da katuttuka wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.
Ma’anar Sufuri
Sufuri hanya ce ta zirga-zirga da jigilar mutane da kayansu daga wannan wuri zuwa wannan wuri, daga unguwa zuwa unguwa, daga gari zuwa gari ko daga kasa zuwa kasa. Sufuri na nufin Zirga-zirgar mutane da sauran kayayyaki daga guri zuwa guri, ta ƙasa kamar titi, titin jirgin ƙasa, ƙafa, da kuma ababen hawa masu inji da waɗanda basu da inji, ta ruwa ta hanyar jiragen ruwa kamar irin su baje, kwale-kwale, da sauransu da kuma ta sama ta hanyar manyan jiragen sama da kuma helikwafta da sauransu.
Ire-Iren
Hanyoyin Sufuri
Ire-iren hanyoyin sufuri sun kasu zuwa gida biyu:
1. Na
gargajiya
a.
Jaki
b.
Doki
c.
Raƙumi
d.
Takarkari
e.
Alfadari
2. Na
zamani
a.
Ruwa
b.
Kwale-kwale
c.
Jirgin ruwa
d.
Mota
e.
Mashin
f.
Jirgin sama
g.
Babur
h.
keke
Amfanin Hanyoyin
Sufuri
· Amfanin Sufuri fanni ne mai matuƙar muhimmanci ga
tattalin arziƙi,
musamman a wannan zamanin da muke ciki wanda zirga-zirgar jama’a da kayansu ke
samar da ƙaruwar
arziƙi a ƙasashe,
kamfanoni da kuma ɗaiɗaikun mutane.
Sufuri a Harkar Kasuwanci shi ne kaɗai kafar da ake kai-komo tsakanin kamfanoni, masana’antu, kasuwanni, kantuna, da sauransu. Saboda haka sufuri ya zamo abu mai matuƙar tasiri a dukkan matakan kasuwanci. Nagartaccen tsarin sufuri, jigo ne wajen ci gaban kasuwanci.
Harkar sufuri kai tsaye ta kanainaye
harkar yawon shaƙatawa
da buɗe
idanu, ita ce kaɗai
kafar da ke ɗaukar
masu yawon shaƙatawa
da buɗe-idanu
daga mazauninsu zuwa gurin da za su ziyarta ciki kuma har da zuwa duniyar wata.
Aikin Aji
1.
Lissafa hanyhoyin sufuri iri-iri guda
biyar.
2.
Kawo muhimmancin hanyoyin sufuri guda
uku?
0 Comments