Ɗalibai su ba da bayanin hanyoyin sadarwa na
gargajiya da na zamani, da kuma sabuwar fasahar sadarwa. A yi amfani da
talabijin da rediyo da bidiyo da kwamfuta da intanet da talagiram da wayar
salula da hotuna wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen
darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.
Ma’anar Sadarwa
Hanyar Sadarwa tsararriyar hanya ce da ake tsarawa ta
aika saƙo ko bayani daga wuri zuwa wani
wuri mai nisa. A kasar Hausa a zamunna da suka shude,
ana amfani ne da kafafen sadarwa ne wajen yada bayanai, sanarwa da isar da
sakon hukuma ko masarauta ga talakawansu.
Ire-iren
hanyoyin sadarwa
1. Na gargajiya
2. Na zamani
3. Na sabuwar fasahar sadarwa
Hanyoyin Sadarwa Na
Gargajiya
Bahaushe yana amfani da kayan kiɗa na gargajiya wajen
isar da saƙonni, wasu lokuttan kuwa yak an yi amfani da sanarwar baki ko yin
yekuwa. Daga ciki akwai:
1.
Kiɗa
2.
Ƙuge
3.
Kwarya
4.
Tambari
5.
Ganga
6.
Ƙaho
7.
Makamashi
8.
Bindiga
9.
Wuta
10.
Hayaki
11.
Ihun yekuwa na baka wato
shela
Hanyoyin Sadarwa
Na Zamani
Bayan zuwan turawa, an ƙara bunƙasa hanyoyin sadarwa inda aka kawo hanyoyi na zamani, ga wasu daga cikin
misalan hanyoyin sadarwa na zamani:
1. Gidan waya
2. Wasiƙa
3. Wasiƙar kan sarki
4. Wasiƙar talagiram
5. Wasiƙar ƙarbi da kanka
6. Kar-ta-kwana
7. Gidan buga waya
8. Wayar tarho
9. Wayar talas wato tangaraho oba-oba
Sabuwar Fasahar
Sadarwa
Bayan wani zamani an ƙara bunƙasa hanyoyin sadarwa a faɗin duniya, inda aka kawo hanyoyin sadarwa na zamani irinsu intane da
wayar salula, waɗannan
hanyoyin sadarwa sun samu karbuwa a faɗin duniya baki ɗaya.
1. Rediyo
2. Talabijin
3. Satilayit
4. Kwamfuta
5. Fas
6. Intanet
7. Wayar hannu wato salula
Aikin Aji
1. Ba da
bayanan ire-iren hanyoyin sadarwa guda biyar da ku ka sani.
0 Comments