Talla

C1.2 Sunayen Hausawa: Marubuci Bello Hamisu Ida

 

Sunayen Hausawa

Ɗalibai su iya kawo sunayen yanka da na rana da na yanayi, su iya tantance sunayen yanka da na rana da na yanayi. A yi amfani da talabijin da rediyo da katuttuka da litattafai da jadawali wajen koya wa ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

 Sunayen Yanka: Sunan yanka na Hausawa, suna ne da ake kiran mutane da shi, bayan zuwan addinin musulunci ƙasar Hausa an riƙa laƙanta wa mutane suna masu daɗi wanda addini ya zo da su.

 Ga misalan wasu daga cikin ire-iren waɗannan sunaye:

1.            Bello

2.            Abdallah

3.            Muhammad

4.            Ibrahim

5.            Aliyu

6.            Abdulkarim

7.            Aisha

8.            Zainab

9.            Fatima

10.         Hafsat

11.         Khadiza

12.         Usman

13.         Umar

Idan aka lura waɗannan sunaye, sunan yanka ne na maza da kuma na mata, wato akwai waɗanda ake kiran maza da su kamar: ‘Muhammad’ da ‘Bello’ haka kuma akwai waɗanda ake kiran mata da su kamar ‘Ummulkhairi’ da ‘Hauwa’u’.

Sunayen Rana: Sunan rana suna ne na gargajiyar wanda ake laƙanta wa mutum wajen yin la’akari da ranar da aka haifi jinjiri, a Ƙasar Hausa ana amfani da irin wannan sunaye ne kafin zuwan addinin Musulumci.

        Ga misalan wasu daga cikin sunayen rana nan:

1.            Ɗanladi                Shi ne wanda aka haifa ranar Lahadi.

2.            Ɗan’asibi              Shi ne wanda aka haifa ranar Asabar.

3.            Ladi                      Ita ce wadda aka haifa ranar Lahadi.

4.            Jumeme                Ita ce wadda aka haifa ranar Juma’a.

5.            Ɗanliti                    Shi ne wanda aka haifa ranar Litinin. 

Sunayen Yanayi: suna ne da ake amfani da yanayin da aka haifi jinjiri a cikinsa, ana laƙanta wa jinjira suna ta hanyar la’akari da yanayin da aka haifi jinjiri.

 Ga misalin wasu daga cikin sunayen yanayi:

Tunau:             Shi ne wanda aka haifa bayan an daɗe ba haihu.

Anaruwa:         Shi ne wanda aka haifa ana cikin yin ruwan sama.

Auta:                Shi ne wanda aka haifa daga ƙarshen haihuwa kuma daga kansa ba a sake haifar wani ba.

Kande:         Ita ce wadda aka haifa bayan an haifi maza da yawa.

Cindo:          Shi ne wanda aka haifa da yatsu shida.

 Aikin Aji

1.     Kawo sunayen hausawa na yanka da na yanayi.

2.     Tantance sunayen yanka da na rana da na yanayi da aka kawo.

3.   Lissafa sunayen ‘yan ajinku da aka sani.

 

Post a Comment

0 Comments