Talla

C1.1 Tsaftar Jiki: Marubuci Bello Hamisu Ida

 

Tsaftar Jiki

Ɗalibai su san ma’anar tsafta su kawo misalan sassan jiki su kawo bayanin yadda ake tsaftace jiki su ba da muhimmancin tsaftace jiki. A yi amfani da hotuna da talabijin da rediyo da kayayyakin tsafta. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

Ma’anar Tsafta

Tsafta tana nufin tsarkake jiki da tufa da abinci da muhalli. Tsafta ita ce kiyaye jiki ko tufa ko abinci ko muhalli daga abubuwan da za su iya cutar da mutum, kamar datti, ko ƙazanta ko ƙwayoyin cuta. Tsafta na da matuƙar muhimmanci a rayuwa, rashin tsafta na kawo cututtuka tare da illata rayuwa. Tsafta ginshiƙi ce wajen samun walwala, da jin daɗin rayuwa da kuma samun kuzarin aiwatar da hidimomin rayuwa. Tsafta tana da muhimmanci a addini, har ma akan ce, ‘Tsafta cikon addini’.

Sassan Jiki

Sassan jiki su ne dukkan ɓangarorin da suka haɗu suke bai wa ɗan’adam damar motsi da aiwatar da abubuwa. Daga cikin waɗannan sassan jiki akwai:

1.           Kai

2.           Kunne

3.           Ido

4.           Hanci

5.           Baki

6.           Hannu

7.           Cinya

8.           Ƙafa

9.           Al’aura

10.       Fatar jiki

Hanyoyin Tsaftace Jiki

Akwai hanyoyin da ake bi a tsaftace kowane ɓangare na jiki, ga kaɗan daga cikin hanyoyin da ake bi wajen tsaftar jiki:

 

1.     A kan taje gashi a wanke shi da ruwa masu kyau da sabulu ko sabulun salo, sannan a shafa masa mai, maza kuwa su kan yi aski don rage yawan suma, mata kuwa su kan yi kitso don yin kwalliya da gyara gashi.

2.     Ba kasafai ake wanke kunne ba, amma a kan ƙwalƙwale shi da auduga sannan a goge shi lokaci-lokaci, rashin goge kunne kan tara datti cikinsa sannan ya riƙa ciwo.

3.     Kullum kuwa in an farka daga barci, a kan wanke idanuwa, sannan a goge su da cire kwantsa, lokaci-lokaci a kan sanya gilashi domin gujewa ƙura.

4.     Duk lokacin da ake wanka ko alwala, a kan fyace hanci saboda kuje wa yawan taruwar majina, sannan in an ji alamar tasono sai a a samu auduga a cire.

5.     Da safe kuwa, a kan wanke baki a goge haƙora da buroshi, haka kuma in za a kwanta barci a kan ƙara wanke baki. Sannan kuwa duk sanda aka yi alwala a kan goge haƙora da magogi wato asuwaki.

6.     Duk sanda za aci abinci, ko aka taɓa wani abu mara kyau, a kan wanke hannu da sabulu ko omo, haka kuma bayan an gama cin abinci sai a sake wanke hannu.

7.     A kan yi wanka a kalla sau biyu ko sau uku a rana, a wanke jiki da duk wata dauɗa da ta taru ko ta yi naso a cikin jiki. Sannan a wanke ƙafafuwa da sabulu da soso. Bayan an yi wanka sai a tsane jiki da tawul sannan a safa mai kafin a saka kaya masu kyau.

Aikin Aji

1.           Yi cikakken bayanin yadda ake tsaftar jiki.

2.           Kawo muhimmancin tsaftace jiki.

 

Post a Comment

0 Comments