Talla

C1.1 Dabarun Tafiyar Da Rayuwa

 

Ɗalibai su iya faɗar dabarun tafiyar da rayuwa, su bayar da bayanin dabarun tafiyar da rayuwa. A yi amfani da jadawali da hotuna da litattafai da CD da talabijin wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.
 
Me Ake Nufi Da Dubarun Tariyar Da Rayuwa
Dabarun tafiyar da rayuwa tsari ne na rayuwa wanda ake ɗora ta bisa wasu tanade-tanade da mutum zai ci gaba a rayuwar yau da kullum.  Rayuwa mai amfani, ita ce rayuwar da zata kasance tana tattare da hakuri da juriya da kuma takawa, ma'ana mika lamari ga Allah makadaici. Kamar in Allah ya hore wa dan'uwanku dukiya ko motoci ko gidaje ko mulki ko yabashi lafiya, to kar ku yi fushi, ku dangana ga Allah madaukakin sarki mai ikon komai da kowa. Kuma kasancewa kowace rayuwa da irin arziki da baiwar da Allah ya yi mata, kuma kowane abu da irin lokacin da Allah yarubuta zaifaru.
 
Dabarun Tafiyar Da Rayuwa
Akwai wasu hanyoyi da ake bi domin tsara rayuwa ta yadda za a samu kyakyawar makoma duniya da lahira, ga wasu daga cikin dabarun tafiyar da rayuwa:
1.      Samun ilimi mai inganci: Ɗaya daga cikin dabarun tafiyar da rayuwa, mutum ya samu ingantaccen ilimi tun daga firemare zuwa sakandare sannan a tafi makarantar gaba da sakantare, ko dai a yi karatun digiri ko makamancin wannan. Haka kuma, yana da matuƙar kyau a sirka karatun muhammadiya da na boko waje ɗaya. Yin ilimi mai zurfi yana ƙara inganta rayuwa.
2.      Bin hanyoyin kiyaye tsaro: Bin hanyoyin kiyaye tsaro da samar da zaman lafiya a cikin ƙasa ɗaya ne daga cikin ginshiƙan tafiyar da ingantacciyar rayuwa. A guji faɗawa cikin faɗace-faɗace ko tashin hankulla ko biye wa abokai maras sa son zaman lafiya.
3.      Guje wa yanayin bala’i ko tarzoma: Gujewa yanayin bala’i ko fitina da tashin hankali ɗaya ne daga cikin abubuwan da ke tafiyar da ingantaciyar rayuwa. Duk inda aka ga fitina to ayi ƙoƙarin kashe ta in za ayi iya yin maganinta, in kuwa tafi ƙarfinku, sai a kai wa hukuma ko nag aba.
4.      Kiwon lafiya: Tattalin lafiya na ɗaya daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen tafiyar da rayuwa. Duk sanda aka ji wani sauyi a cikin jiki to a garzaya asibiti ko a tuntuɓi malaman lafiya. Kar a zauna gida da ciwo ba tare da zuwa asibiti ba.
5.      Dogaro da kai: Neman sana’ar yi da dogaro da kai ya hanya ce ta tafiyar da rayuwa cikin inganci. A guji maula da neman abu wajen wani musamman in aka samu damar gudanar da sana’a kar ayi wasa da ita.
6.      Kyautata sana’ar zamani: Sana’o’in hannu na zamani suna taimakawa sosai wajen tafiyar da ingantacciyar rayuwa. A koyi sana’o’in hannu kamar su gyaran waya, amfani da komfuta, sarrafa intanet, kirkirar manhajar wayar hannu, ɗinki, tireda da sauransu.
7.      Kyakyawar mu’amala:  Kulla kyakyawar mu’amala da mutanen kirki hance da tafiyar da ingantacciyar rayuwa, a guji abokai maras sa kirki, sannan a guji faɗa da abokai ko makwabta ko yan’uwa ko abokan zaman aji.
8.      Ɗa’a da biyayya: Yin ɗa’a da biyayya ga magabata da iyaye da abokai da malamai hanya ce da ke inganta rayuwa.
9.      Guje wa cin hanci da shan miyagun ƙwayoyi: Idan an samu wani aiki, sai a guji cin hanci da rashawa da shan giya ko miyagun ƙwayoyi, duk waɗannan munanan ɗabi’u ne da ke kai mutum cikin halaka.


Aikin Aji
1.      Faɗi dabarun tafiyar da rayuwa guda biyar?
2.      Yi taƙaitaccen bayani akan dabarun tafiyar da rayuwa?

 

 

Post a Comment

0 Comments