Ɗalibai su bayyana wasu miyagun kwayoyi, su tantance ire-iren miyagun ƙwayoyi. A yi amfani da talabijin da rediyo da bidiyo da hotuna da katuttuka da litattafai wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.
Ma’anar Miyagun Ƙwayoyi
Kwaya
magani ce da ake amfani da ita wajen magance cututtukan da kan addabi jikin
mutum. A ganin wani masani mai suna Caroll (1989), kwaya na nufin wani
sinadari, wanda da zarar ya shiga jikin mutum zai canja fasalin aikin jikin da
tsarin gudanarwarsa. Don haka ma’anar tu’ammali da kwaya na nufin sha, yin
allura ko zukar hayakin duk wani sinadari ba da izinin likita ba, ko kuma
amfani da wani magani ba da nufin magance wata cuta ba.
Tun
asali, ita kwaya magani ce da ake amfani da ita wajen magance cututtukan da kan
addabi jikin mutum. Kwaya na nufin wani sinadari, wanda da zarar ya shiga jikin
mutum zai canja fasalin aikin jikin da tsarin gudanarwarsa. Don haka ma’anar
tu’ammali da kwaya na nufin sha, yin allura ko zukar hayakin duk wani sinadari
ba da izinin likita ba, ko kuma amfani da wani magani ba da nufin magance wata
cuta ba.
Bayyana Wasu
Miyagun Ƙwayoyi
A
lokacin da mutum ya kasance ba zai iya rayuwa ba tare da ya sha wani sinadari
ba, to za a iya cewa ya kamu da cutar shan kwaya, wadda haka na faruwa ne
sakamakon jimawa a cikin shan magani ba da izinin likita ba, ko ba da nufin
magance wata cuta ba. Idan an shiga wannan yanayin, ke nan an samu yanayin da
zai haifar da matsalar mutum ya kasa barin sha da kuma sauran matsaloli da kan
iya kawo masa cikas cikin al’umma, a wurin aiki ko a makaranta. Akalla dai a
nan, ana nufin sabo da kwaya shi ne mutum ya dogara da shan wani magani ko
sinadari duk tsawon rayuwarsa.
Hanya mafi sauki da za a bi a lalata kowace irin
al’umma, ita ce ta hanyar jefa matasa cikin shaye-shayen miyagun kwayoyi, idan
suka siffatu da shaye-shaye, za su kasance gurbatattu, lalatattu, su jefar da
neman ilimi, ba za su iya tsinana wa kansu komai ba a rayuwa, inda daga karshe
kuma za su kasance bayin dillalan kwaya.
A kiyayi shan kwaya, domin kuwa tu’ammali da
miyagun kwayoyi kan ingiza mutum cikin tunanin cewa yana cikin Aljanna, alhali
cikin jahannama yake.
0 Comments