Talla

B.2.3 Gajerun Labarai

 

Gajerun Labarai

          Ɗalibai su bayar da labaran gargajiya, su karanta labaran gargajiya da na zamani, su fito da darussan labaran gargajiya ko na zamani sannan su fito da bayania daga labaran. A yi amfani da hotuna da taswira da rediyo da kaset da rikoda wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

Labaran Karambana Ko Kaga Dokin Sarki Na Uku

Warri wani gari ne da yanzu yake a cikin Jihar Delta, ana kiran garin da ‘Birnin Mai’, garin yana da arziƙin ma’adanin mai da aka fi sani da fetur. Ana ce masa ‘birnin mai’ saboda ya shahara sosai wajen haƙo man fetur. Kamar kwal, Fetur ma wani ma’adani ne wanda ake kira da ɗanyen mai. Ana samun man fetur a wurare da yawa a duniya, kamar a cikin ƙasar Najeriya, ana samun ɗanyen mai a garuruwa: Delta, Riɓers, Imo da Cross Riɓer. Ana samun mai a ƙarƙashin duwatsu da ƙarƙashin ƙasa ko ƙarƙashin teku.

Suna cikin tafiya sai Karambana ya tambayi Bawa ya ce,

“Shin me yasa ka ke biyayya ga turawa?”

Bawa ya kale shi sannan ya ce,

“Saboda suna da abun mamaki”

Karambani ya yi karab ya ce,

“Shin sun fi jakar ƙudiri abubuwan mamaki ne?”

Sai bawan ya ce,

“Bari mu isa ka ga abubuwan mamaki da suke ƙerawa”

Suka ɗanyi shiru, sannan bawa ya ce,

“Su ne suka fara haƙo Fetur”

Karambana ya ce,

“wace irin hallita ce kuma fetur?”

Bawa ya ce,

“Babu wanda zai iya cewa ga haƙiƙanin asalin fetur,an dai ce fetur ya samu ne sanadin wasu ƙwayoyin hallita da ke rayuwa a cikin ruwa”

Ya ɗanyi shiru, bayan sun haye wani kwazazzabo sai ya ci gaba da cewa,

“In waɗannan halittu sun mutu sai su nutse ƙasa, yashi ya lulluɓe su. Bayan tsawon lokacin waɗannan matattun halittu da ba su samun tattaciyar iska sai su canza su zama fetur”.

Lokacin da suka shiga garin Warri sai su Karambana suka saki baki suna kallon abubuwan mamaki, suka ga yadda ake haƙo ɗanyen mai a ƙasa ta wata hanya ta musamman wace ake saka ƙarafuna masu kwararo sannan ayi burtsatsen man. Daga farko ana tura dogayen ƙarafunan dogaye masu bututu a cikin ƙasa sai ya kai inda man fetur yake, sai a yi amfani da wani famfo na musamman da za a turo man ta cikinsa.

Bayan sun sauka masaukin wannan bature sai Bawa ya ja su suka shiga gari don su buɗe idanuwansu. Sun ga abubuwan mamaki da yawa, sun ga yadda ake haƙar mai da yadda ake sarrafa shi.

Hakar mai abu ne da ke son hikima da fasaha da kwarewa, sai an koyi yadda ake haƙar mai sannan ake farawa. Ana dafa mai kafin a fitar da abubuwan da ke cikinsa, wannan hanya ta musamman ta dafa fetur domin fitar da abubuwan iri daban-daban ita ce ake kira tace fetur, wurin da ake rarrabe waɗannan kayayyakin shi ake kira matatar mai. Yanzu akwai manya-manyan kamfanoni a ƙasar Najeriya da suke aikin haƙar mai ba dare, ba rana.

Bayan su Karambana sun ga yadda ake haƙo man fetur an tace shi, an fidda abubuwa da dama, kamar: fetur, iskar gas, kananzir, man inji, man shafa da kwalta da ruwan ammoniya (Iska ce mai ɗoyi) daman hana ƙarfe tsatsa da roba da takin zamani daga wanda ake fitarwa daga dussar man fetur. Sai suka buƙaci baturen ya sanar da su ilimin sama da kuma taurari don su koma gida su ba Malam labarin abinda bai sani ba, wanda jakar ƙudiri ba zata iya samarwa ba.

 


Muhimman Kalmomi

Fetur                              Wani sinadari ne wato ma’adani da ake zubawa mota ko mashi ko inji wanda ake haƙowa sannan a sarrafa, a cikinsa ana samun abubuwa da dama.

Man shafa                       Ana samunsa daga man fetur, in an sarrafa, ɗanyen man fetur, akan fitar da abubuwa ciki har da man shafa.

Roba                              Sinadari ne da ake samu daga ma’adanin fetur, ana yin robobi da shi.

Iskar gas                         Sinadari iska ne da ake fitarwa daga ɗanyen man fetur, ɗaya ne daga cikin albarkatun ƙasa.

Kanazir                           Sinadari ne da ake fitarwa daga ɗanyen man fetur, shi ma ɗaya ne daga cikin albarkatun ƙasa.

Man inji                         Sinadari ne da ake fitarwa daga ɗanyen man fetur, shi ma ɗaya ne daga cikin albarkatun ƙasa.

 

Labarin Bafilatani Da Madarar Klin

Akwai wani Bafulatani da yake zuwa sayayya wani kanti kullum in ya ga omon klin sai ya ɗauka garin madara ne. Wata rana sai ya fashe asusunsa, ya je wannan shago ya ce a bashi madara. Da komawarsa gida, sai ya haɗa shayi sannan ya zazzage wannan garin madara cikin shayinsa. Amma sai ya raina yawan madara da ke cikin ledar madarar da ya saya. Ya lura da cewa duk sanda aka zazzage garin omon klin yana da yawa sosai.

Sai ya ɗauki sandarsa ya koma shagon, ya nuna mai shago da sanda ya ce,

“Kai da nasshe a bani wancan mai yawa? Sai ka bani ɗan kaɗan don cuta?”

Daga nan mai shago ya ɗauko omon klin ya miƙa wa bafillatani, shi kuwa ya koma gida ya zazzage omon klin cikin shayinsa. Yana fara shan shayi, sai ya ji zafi a cikinsa da ƙirjinsa. Can da zafi ya yi yawa sai Bafulatanin nan ya yi ihu, ya sake koma kanti.

Sai ya ce da mai shago: “Wannan wasshe irin madara ki ka bani mai ƙarfi haka?

Sai mai kanti ya amsa masa da cewa ai ba madara bace omo ne. Da Bafilatani ya ji an ce abin da ya sha ba madara ba ce omo ne, sai ya ce:

“Wayyo na mutu”

Aka ce da shi me ya faru? Sai ya ce:

“Wannan omon ci na zuba a cayin nan na ca, ji nake madara she. Do Allah ku kai ni asibiti”.

 

Muhimman Kalmomi

Klin                                nau’i ne na omo wanda ake wanke sutura ko kaya da shi.

Madara                           sinadari ne da ake yin shayi da shi, ana samar da shi daga madarar shanu ko waken suya.

Shanda                           icce ne wanda Fulani ke riƙewa bisa al’ada.

Asibiti                            wajen da ake kai maras sa lafiya domin likita ya duba su a ba su magani.

Shago                             wajen da ake sayar da kayan abinci da saura abubuwan amfanin yau da kullum, a kan ce kanti ko shago.

Bafillace                         Fulani ƙabila ce da ke ƙunshe da al’adu da dama, bafillace namiji ne wanda ya fito daga ƙabilar Fulani.

 Tambayoyi

Cike waɗannan gurabe:

1.     Warri wani gari ne da yanzu yake a cikin Jihar ______________?

2.     Ana kiran garin da _________________________?

3.     Kamar kwal, Fetur ma wani _____________________?


Post a Comment

0 Comments