Talla

B2.3 Gabatar Da Karya Harshe: Marubuci Bello Hamisu Ida

 

Gabatar Da Karya Harshe

Ɗalibai su iya karya harshe, su kawo mislan karya harshe. A yi amfani da rediyo da talabijin da kaset-kaset da rikoda wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshe darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

Ma’anar Karya Harshe

Karya harshe wata dabara ce ta sarrafa harshe a kuma karyashi, ta hanyar maimaita wasu harufan cikin hawa ko saukar murya don gwananta a cikin sarrafa harshen. Karin harshe hikima da ake amfani da ita wajen sarrafa harshe, domin koya wa yara iya magana da kuma iya sarrafa harshensu.

Ana nuna hazaƙar yaro wajen gwada shi ya faɗi wasu kalmomi masu sarƙaƙiyar hawa da saukar murya, inda zai maimaita da sauri, da sauri.

Hanyoyin Karya Harshe

Gagara-gwari: Wannan shi ne wanda ake samun luguden kalmomi, masu sautuka iri ɗaya. A lokacin da mutum yake faɗarsu da sauri, to sai ya ɓace ya kasa faɗarsu daidai.

 Misalan irin waɗannan sun haɗa da:

 

‘Matar ƙona-ƙota’.

‘ƙona-ƙota yana gida?’

‘Baƙon ƙona-ƙota, ƙona-ƙota ya je gona’.

‘To, ke matar ƙona-ƙota ba ni aron ƙotar ƙona-ƙota in ƙona’.

‘Ni matar ƙona-ƙota, ban ɗauko ƙotar ƙona-ƙota na ƙona ba, sai kai baƙon ƙona-ƙota zan bai wa ƙotar ƙona-ƙota ya ƙona?’

 Wannan ƙarya harshe, an yi anfani da luguden kalmomi masu ƙunshe da baƙin ‘ƙ’ waɗanda idan har za a riƙa faɗarsu da sauri-sauri, to dole ne a kuskure ko a kasa faɗa baki ɗaya.

 Ga wani misalin karya harshe:

Da kwaɗo da ƙato suka je yawon ƙoto, ƙato ya ga ƙoto, kwaɗo ya ya ƙoto. suka yi ƙatako-ƙatato. Wa zai ƙwace wa wani ƙoto? ƙato ne zai ƙwace wa kwaɗo ƙoto, ko kuwa kwaɗo ne zai ƙwace wa ƙato ƙoto?

 Ingiza Bami: Irin wannan karya harshe shi ne wanda idan mutum ya yi ta maimata shi da sauri, to sai ya faɗi wani abin daban na kushe kansa ko kuma ma ya yi batsa.

 Misali:

Na hau kace:

Ga bayanin yadda karya harshen yake kasancewa:

Ana nuna cewa akwai wata bishiya, da ake cewa bishiyar

kace. To idan mutum ya yi ta maimata cewa,

Ya hau wannan bishiya, to daga ƙarshe sa ya ƙare de cewa

‘Ya haukace’,  wato taɓin hankali.

Ga wani misali:

‘Na yi caraf na cafke gemun ragon Baba na layya’.

Idan aka yi ta maimatawa da sauri, to sai a ƙare da cewa,

‘An cafke gemun Baba’

Maimakon, ‘gemun ragon Baba’.

Aikin Aji

1.    Kawo hanyoyin karya harshe?

2.    Kawo yadda ake karya harshe ta hanyar amfani da waɗannan Karin harshe:

Ƙato ya yi ƙoto

Kwaɗo ya yi ƙoto

Na hau bishiyar kace


 

 

Post a Comment

0 Comments