Talla

B2.1 Gajerun Waƙoƙi

 

Gajerun Waƙoƙi

Ilimin Zamani

Gishiri im babu kai ba miya,

Ilmi mai gyaran zamani,

 Jama’armu ku jawo hankulanku,

Ku lura da halin zamani.

 Iko, mulki, ƙarfi duka,

Na ga wanda ya ƙaddar zamani.

 Ilmi shi ke gyaran ƙasa,

Har a san ta a awannan zamani.

 Babu jin kunya gun alimi,

Jahili shi ke ta wuni wuni.

 Yadda kaska ke tsotson jini,

Haka jahilci gun zamani.

 Da tsiya da talauci duk kun sani,

Gun da jahilci ya yi sansani.

 Wa’azummu ga mai karɓa duka,

Masu murnar gyaran zamani.

 Masu son lardimmu ya ɗaukaka,

Bisa kan juyawar zamani.

 Kar su fara faɗar da-na-sani,

Da mun yi karatun zamani.

Maza mata ku yi azzama,

Mai gemu da yaro ƙanƙane.

Muhimman kalmomi a cikin waƙar ‘Ilimin Zamani’:

Kalmomi

Ma’anarsu

Gishiri

Sinadari ne wanda ake sa wa abinci domin a samu zaƙin miya.

Zamani

Lokaci

Hankali

Amfani da fahimtar da Allah ya ba mutum.

Lura

Kallo abu da idon basira

Mulki

Sarautar wani waje

Ƙarfi

Nuna iko da isa

Duka

Komai da komai

Ƙadddara

Abun da Allah ya hukunta zai samu

Ƙasa

Yanki ko lardi

Jahili

Marar ilimi

Wuni

Daga Safe zuwa dare

Tsotson jini

Jawo jinin jiki ko zuƙo jinin jiki.

Kaska

Ƙwaro ne da ke maƙalewa a jikin dabbobi musamman kare ko sa saniya.

 

Mu Yaƙi Jahilci

Ya alla ka taime mu,

Kai mana babban tsari da jahilci.

 

Zaman jama’a cikin duniya,

Ba ya kyau idan da hajilci.

 

Zalunci gami da lalaci,

Duka mai haddasa su jahilci.

 

Sata da fashi da in caca,

Duk mai haddasa su jahilci.

Tsumma, kwarkwata, tsiya, yunwa,

Duka mai haddasa su jahilci.

 

Rashin haɗa kai, yawan hargitsi,

Duka mai haddasa su jahilci.

 

Yawan tankiya ga ‘yan iska,

Duka mai haddasa su jahilci.

 

Hawannafsi, ƙin zumunta mun,

San mai haddasa su jahilci.

 

 

Yawan fankama ga girman kai,

Duka caffarsu na ga jahilci.[1]


Muhimman Kalmomin A Cikin Waƙar

Kalmomi

Ma’anarsu

Ya Alla

Ya Ubangiji Sarkin hallita

Taime ke mu

Taimako wato neman agaji

Babba

Na garima

Tsari

Kariya

Jahilci

Rashin ilimi

Zama

Sauyawa daga wani abu zuwa wani abu

Zalunci

Ƙeta, kwace wani abu da ba na ku ba.

Gami

Haɗi da wani abu.

Lalaci

Rashin tashi a nemi halas

Hassada

Jin haushi don Allah ya ba wani abu ga wani ɗan’uwanku.

Sata

Ɗauke abun wani ba tare da ya sani ba.

Fashi

Ɗauke abun wani da ƙarfi da hanyar nuna makami,

Caca

Sanya kuɗi don aci wata ƙauta.

Tsumma

Lalatattun kaya.

Tsiya

Rashin abun kai, talauci.

Yunwa

Rashin cikin abinci.

Rantsuwa

Gitta rai don samun wani abu.

Ƙarya

Faɗin abun da ba gaskiya ba.

Caffa

Kai sukar wani ko wata.

 Aikin Aji

Rera waƙoƙin da aka nazarta a cikin aji.

Ba da ma’anar muhimman kalmomi guda biya.

 


[1] An ciro waƙar ‘Ilimin Zamani’ da waƙar ‘Mu Yaƙi Jahilci’ daga littafin: ‘Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja’.

Post a Comment

0 Comments