Adon Magana
Ɗalibai su san ma’anar adon magana, su yi bayanin adon magana da misalan
adon magana. A yi amfani da katuttuka ɗauke da kalmomin adon Magana da littafin ƙamus da jadawalin kalmomin adon magana. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.
Ma’anar
Adon Magana
Adon magana salo ne na yin magana taƙaitacciya kuma dunƙulalliya wadda ke ɗauke da ma’ana mai yawa da isar da saƙo cikin hikima. Ana
yin amfani da adon Magana domun ayi nuni, gargaɗi, yabo, ko ƙarfafa guiwa. Adon magana ana yi wa kalmomi ado ne ta hanyar ƙara wasu kalmomin domin ayi nuni cikin hikima da fasaha.
Bayanin Adon
Magana
Adon magana amfani ne da kalmomi inda ake yi masu
ado domin a samu ingantaccinyar Hausa sannan ayi magana cikin harshen da hikima
ta yadda mai sauraro zai fahimci zancen da ake yi, akan taƙaita kalmomi ne ayi amfani da wasu kalmomi domin
ayi wa zancen ado da kwaskwarima. A kan yi Habaici, Zambo, Zaurance da sauransu
a cikin zantuka da kuma rubutun Hausa ta hanyar amfani da adon magana.
Misalin adon magana cikin zance:
1.
Sani yana yin kyauta ne da hannun dama ya karɓa da hannun haggu.
2.
Alhaji mai gani har hanji kenan, komai yana ankare da shi.
3.
Wannan ai ragon malam ne, ga mai ga arha.
4.
Ina zan samu takalman saye masu sauƙi kamar tuwon suna?
5.
Kan sa kamar an matse rama.
Misalin
Adon Magana
Ga
wasu daga cikin misalan adon magana:
1.
Idon
zakara
2.
Hannun
ruwa
3.
Ƙarkon
kifi
4.
Dukan
ciki
5.
Cin
hanci
6.
Cin
fuska
7.
Cin
zarafi
8.
ci-ma-zaune
9.
Zaman ‘yan marina
10. Kafircin mage
11. Cinikin kifi a ruwa
12. Shahadar ƙuda
13. Farke laya
14. Gadar zare
15. Gashin zuma
16. Harbin iska
17. Kukan kura
Aikin Aji
1.
Yi
bananin adon magana?
2.
Kawo
misalan adon magana?
3.
Fito
da ma’anar adon magana?
0 Comments