Talla

B1.1 Karatun Gajerun Wasanin Kwaikwayo


Ɗalibai su karanta was an kwaikwayo su bayyana yadda kowane ɗan wasa yake fitowa a cikin wasa. A yi amfani da litattafai da rediyo da talabijin da bidiyo da sidi. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

 Karanta Littafin Wasan Kwaikwayo

Wasan kwaikwayo, kamar yadda sunan ya nuna, wasa ne da ake gina shi kan wani labari, ko wata matsala ta rayuwa da ake son nusarwa ga jama’a don ilmantar da su daga hanyar da ta dace da rayuwa, cikin siffar yakini wato zahiri.

Wasan kwaikwayo a Ƙasar Hausa yana da nau’o’in sanannu guda biyu, ya rabu zuwa nau’o’I kamar haka:

  1. Wasannin kwaikwayo na Gargajiya
  2.  Wasannin kwaikwayo na Zamani

 Wasannin Kwaikwayo Na Gargajiya

Wasannin kwaikwayo na gargajiya wasanni ne da Bahaushiyar al’ada ta yarda da su, waɗanda daga cikin wasannin akan yi  su, ko a gabatar da su a kowane lokaci.

Wasu kuma daga cikinsu akwai lokutan da ba a yin su, wasu kuma akan gabatar da su shekara-shekara kuma akan yi su a wasu lokutan bukukuwan al’ada. Misali a lokacin watan Azumi akan yi wasan tashe da kuma lokutan kaka inda akan yi wasan buɗar dawa da cin tumu da sauransu.

 Wasannin Kwaikwayo Na Zamani

Rubutaccen wasan kwaikwayo, da yake a rubuce ake samar da shi, an san lokacin da aka fara yin sa. Shi rubutaccen wasan kwaikwayo kuwa mai gajeren tarihi ne, in an kwatanta shi da sauran ɓangarori na adabin zamani na Hausa. 

 Gajeren Wasan Kwaikwayo na Gargajiya

 Wasan Buɗar Dawa

Wasan Buɗar dawa wasan kwaikwayo ne da Hausawa ke yi shekara-shekara don neman tsari daga cututtukan shekara da kuma sanin abinda shekarar za ta kawo. Bokaye da Maharba da Manoma su suke shugabantar wannan buki. Anayin wannan biki ne bayan ruwan damina ya ɗauke da wata huɗu. Idan wannan wata na huɗu ya kama ranar sha huɗu ake  gudanar da wannan wasa.

Ana buƙatar kayan kiɗa da bushe-bushe da raye-raye wajen wasan buɗar dawa abin lura anan wasan kwaikwayo da ake yi adandamali shi ma ana aiwatar dashi da kiɗe-kiɗe da bushe-bushe da raye-raye a yayin aiwatar da shi.

 
Yadda Ake Yin Wasan Buɗar Dawa
Yanda ake aiwatar da shi wannan wasa na Buɗar dawa shi ne dazarar damina ta wuce, bayan wata huɗu ake yin wannan wasa, tun kafin lokacin za’a sanar da mutanen gari da na ƙauyuka, wato dai ana karaɗe gari ne da shela tare faɗin ranar da za ayi. Haka zalika za a fitar da ƙauyen da za a gudanar da wasan tare da dajin da za a je.
 
Waɗanda kuwa su ke lissafin watannin ɗaukewar ruwa da ranakun wata su kan san ranar tun kafin ta zo. Tun kafin ranar jama’a za su yi ta taruwa a garin da za ayi Buɗar dawar, idan ana gobe za ayi wasan (bukin), da la’asar sai manyan Manoma da Bokaye da Maharba a karkashin shugabancin babbansu su fita su kewaye dajin da za a yi farauta a cikinsa.
 
A ranar da zaayi wasan da sassafe, sai manya da sauran jama’a da makaɗa su yi ta kaɗe-kaɗe da bushe-bushe. Idan an fita duk dabbar da aka fara cin karo da ita sai a kashe a kawo a gaban manya, bayan nan sai ayi al’adar da za su yi sai susa a feɗe dabbar da aka yo farautar a gaban jama’a, da zaran an feɗe sai a fito da tumbinta sai manyan su zauna nazarin kayan cikin tumbin don su gane abinda  zai faru a shekarar a dalilin dubiya  da za suyi  ma tumbin da nazarin sa.
Idan sun sami ƙwari ko tsutsotsi a cikin tumbin sai su lura idan ƙwarin nan matattu sun fi ya wa sai su ce a shekara mai zuwa za ayi mace-mace. Idan kuwa ƙwarin ba matattu ba ne amma duk ba su da kuzari kamar marar sa lafiya sai su ba da labari shekara mai zuwa za ayi cututtuka amma ba mutuwa da yawa.
 
Idan kuwa suka tarar da tumbin akwai ruwa da yawa a cikinsa sai a faɗa musu cewa wannan shekarar za’a samu ruwa  da yawa, idan ya kasance a katarar tumbin ba ruwa sosai sai su ba da labarin a shekarar za ayi fari. Wannan shi ne misali kadan da ga cikin irin abubuwan da su ke faɗa.
 
Bayan an gama karanta abin da ke cikin tumbin, sai kuma a shiga rabon naman zuwa ƙungiyoyin mutane. Kowa zai ƙoƙarin ya sami naman dabbar nan kome ƙanƙantarsa, wanda ya sami naman sai ya kai gida a saka cikin girkin abincin gidansa. Irin wannan abinci idan an gama ana raba ma dangi kowa ya samu ya ci, sun ce cin irin wannan abinci  da ake yi da wannan nama zai tsare wanda ya ci daga sharrin cututtuka da masifun wannan shekara, irin wannan wasa ya yi sauƙi bayan zuwan musulunci amma har yanzu ana yin sa a birnin Ƙwanni cikin Jamhuriyar Niger.
 
Yadda Kowane Ɗan Wasa Ke Fitowa
Mutanen da ke aiwatar da wasan Buɗar dawa su ne kamar haka:
1.      Manoma
2.      Mafarauta
3.      Bokaye
4.      Mutanen gari
 
Aikin Aji
1.      Karanta wasan kwaikwayo na uwar gulma.
2.      Ba da bayanin yadda kowane ɗan wasa yake fitowa a wasa.
3.      A shirya wasan kwaikwayo a cikin aji, a lura da yadda ake fitar da yan wasa.

 

Post a Comment

0 Comments