Gajeren Rubutaccen Wasan Kwaikwayo
A darussan da su ka gabata, an fahimci abin da ake nufi da wasan ƙwaiƙwayo, an fahimci ma’ana da rabe-raben wasan ƙwaiƙwayo tare da misalin rubutaccen wasan ƙwaiƙwayo. A wannan darasi, ɗalibai su fahimci jigon wasan ƙwaiƙwayo, da yadda ake jera manya da ƙananan ‘Yan wasa, a jagoranci ɗalibai wajen yi masu bayanin wani wasan ƙwaiƙwayo na littafi, kamar wasan ƙwaiƙwayo na ‘Uwar gulma’ ko wasan ƙwaiƙwayo na ‘Marafa’. A karanta litattafan wasan ƙwaiƙayo tare da yi masu bayanin jigo da ‘Yan wasa tare da fiddo da darasin da ke cikin wasan. Ayi wa ɗalibai tambayoyi don a tabbatar da cewa sun fahimci darasi. Ayi amfani da litattafan wasan ƙwaiƙwayo da rediyo da talabijin da rikoda da kaset.
‘Yan
Wasa
Jerin sunayen
‘yan wasa da halayensu:
Manyan ‘Yan Wasa
Ɗanliti: Babban ɗan
wasa ne, shi ne mijin Talatu kuma mahaifin Sarai, Asabe da ‘Yar auta, yana da ƙoƙari
sosai wajen tura ‘ya’yansa makaranta.
Talatu: Babbar ‘yar wasa ce, mace mai son kuɗi,
kullum tana tura ‘ya’yanta talla domin su nemar mata kuɗi,
bata son suna zuwa makaranta.
Yar
auta: Babbar ‘yar wasa ce, bata son
zuwa makaranta, daga ƙarshe rayuwarta
ta lalace sanadiyar yin talla.
Mai-rogo: Babban ɗan
wasa ne, mutum ne mugu mai ɓata tarbiyar
yara.
Ƙananan ‘Yan Wasa
Sarai:
Ƙaramar
‘yar wasa ce, ita ce babbar ɗiyar Malam Ɗanliti,
tana son karatu, tana zuwa makaranta.
Asabe: Ƙaramar
‘yar wasa ce, tana son zuwa makaranta amma mahaifiyarta tana tursasa mata zuwa
talla.
Hedimasta: ƙaramin
ɗan
wasa ne, shi ne shugaban makaranta ne, wanda ke kula da ɗalibansa.
Malami
na ɗaya: Ƙaramin ɗan
wasa ne, malami ne mai sa ido a kan rayuwar ɗalibansa.
Malami
na biyu: Ƙaramin
ɗan
wasa ne, Malami ne mai sa ido a kan rayuwar ɗalibansa.
Jiƙamshi: Ƙaramin
ɗa
wasa ne, mutum ne mai sa ido ga rayuwar mutane.
Matsala: ƙaramin
ɗan
wasa ne, yana saida rake, mutum ne wanda bai damu da abinda wasu ke aikatawa
ba.
Taken
Wasa: Matsalarmu a Yau
A wannan wasa
mai taken ‘Matsalarmu a Yau’ mai fitowa uku wanda ya bayyana jigon aibun talla
da rashin zuwa makaranta, wasan yana ɗauke da ‘yan
wasa guda goma sha ɗaya. Za mu ga yadda wani magidanci kulum
ya ke ƙoƙarin
tura ‘ya’yansa mata makaranta, amma sai uwarsu ta tura su talla, inda daga ƙarshe
aka lalace wa ‘yar autarta rayuwa.
Fitowa
Ta Farko
(A
Gidan Malam Ɗanliti)
Ya fito daga
turakarsa, sannan ya yi gyaran murya, ya jirkice tare da saɓe
babbar rigarsa gefe ɗaya, ya sanya hannu aljihu ya fiddo kuɗi.
Ɗanliti Sarai, asabe, ‘yarauta (ya kwalla masu
kira) ku fito ku tafi makaranta mana, har ƙarshe
bakwai da minti biyar ta yi, bana so kuna lattin zuwa makaranta.
Talatu
(Tana daga cikin ɗakinta
ɗaga
murya) ai kam, Malam da har na ce yau kar su je makaranta, ina so in aike su
wani waje ne.
Ɗanliti Wace irin magana ce wannan marar amfani,
kin taɓa
ganin inda yaro ya yi rayuwa ba karatu? To bana son irin wannan magana marar
amfani.
Ɗanliti (ya ɗan yi
shiru yana shaƙar
iska) ki fito.
Sarai (Ita ce babbar ‘yarsu, ta fito cikin
sauri, riƙe da
jakar makarantar ta) baba ni har na gama shiryawa.
Ɗanliti (Ya fiddo kuɗi, ya
miƙa
mata) ga kuɗin
tara, ki tambayi malamanku ko akwai litattafan da ku ke buƙata a
saya na karatu.
Sarai To baba, mun gode (ta saɓa
Jakarta, ta yi gaba).
Ɗanliti Ku kuwa in kun gama duminiyar sai ku bi
sahunta, ku Tabbata kun je makaranta da wuri. (Ya shiru takalmansa ya yi gaba)
Talatu
(tana guna-gunai) Muguwar yarinyar
can mai farar ƙafa,
yanzu ta sa dole sai anyi jibgaron tire ɗaya.
Asabe da ‘Yar auta suka fito daga ƙuryar
ɗaki,
sanye da rigar kanti da atamfa, sun saɓa wani yamaɗiɗin
gyale, sannan suka nufi inda aka aje tiren tallar kayan miya.
Asabe Inna
ina dawowa zan tafi makaranta.
Talatu Wannan kuma ke ta shafa, ni kam
abinda ya dame ni, ki tabbata kin sayar da komai. (ta ɗanyi
shiru) ai wannan talla da malam ya raina da ita ce zan cika wa kowace daga
cikinku ɗakinta
da kayan alatu, amma banda waccan mai farar ƙafar.
Talatu Wa ya ce masa akwai wata moriya a
karatun boko? kullum zai addabi rayuwarmu da zuwa makaranta.
‘Yar
auta (Ta fito bayan ga gama yin ja
gira da jambaki, ta yafa gyale sannan ta ɗauki
tire) Inna su ne ke rufa wa baba baya a kan karatun nan, ni ko saurararsa bana
yi, yadda na tsani makarantar nan kamar mutuwata.
Talatu Ka ji ɗiyar
albarka, ai shi yasa ki ka fi su ƙashin arziƙi.
Kayan ɗakinki
sai ya fi na kowa.
Dukkansu suka ɗauki
tire, suka yi waje, suna bin gida-gida suna faɗin “A
sai kayan miya” “za ku sayi kayan miya”.
Fitowa
Ta Biyu
(A
Cikin Makarantar Firamare)
Bayan an gama
asambile, kowa ya shiga aji, malamai ana ta darussa, sai Hedimasta ya kira wasu
amintattun malamansa waɗanda basu da
darasi a lokacin.
Hedimasta Duk da yake iyaye na bakin ƙoƙarinsu
wajen tura yara makaranta, amma sai a samu yara da yawa suna laɓewa
in an turo su makaranta. Don haka ina so ni da ku mu bi lungu-lungu da saƙo don
kamo ɗaliban
da suke ƙin
zuwa makaranta.
Malami
na ɗaya Ranka shi daɗe,
rannan ma na ga ɗiyar gidan malam Ɗanliti
tana talla a lokacin makaranta, kasan ni ke kira masu rigista, sau da yawa bata
zuwa makaranta.
Malami
na biyu Yana bakin ƙoƙarinsu,
amma ba su samu uwa ta gari ba, ita ce ke ɗora
masu talla.
Hedimasta In kun gan su yau
sai ku tafo da su makaranta.
Dukkansu suka warwatsu cikin gari, don
kamen yaran da basu zuwa makaranta.
Fitowa
Da Uku
(Cikin
Unguwa)
‘Yar
auta A sai kayan miya:
citta, karamfani, albasa, tarugu, busasshen tattasai, busashen tumatus,
daddawa, kuka, magi da manja.
Mai-rogo (Yana zaune bisa dakalin ƙofar
gidansa, ya kanne idonsa ɗaya wanda yake
gani dashi, yana kallon ‘Yar auta tana talla) shin waccan ba ɗiyar
gidan Malam Ɗanliti
ba ce?
Matsala (Ya ƙura
ido sosai) eh, ita ce, ai ita kullum bata zuwa makaranta, sai talla.
Ya
tashi daga saman dakalin, sannan ya nufi wajen sana’arsa inda yake saida rake,
bayan ya ɗan
fere wani raken sai ya gutsura sannan ya ci gaba da ɓantala
yana sha, hankalinsa ya tafi. Shi kuwa Mai-rogo hankalinsa na wajen ‘Yarauta,
lokacin da ta ƙaraso
sai ya ce ta shiga gidansa ta kai cefane, tana shiga sai ya bi sawunta.
Jiƙamshi (Yana zaune can daga gefe yana
shan inuwa, ya ga duk abinda ya faru tsakanin Mai-rogo da ‘Yar auta) Kai
Mai-rogo bai kyauta ba, to sai na kai gulmarsa wajen Hedimasta, duk abin da
yake aikatawa a cikin garin nan ina sane da shi.
Malami
na ɗaya (Ya karyo kwana bisa kekensa, yana tafe yana
rarraba idanuwa, daidai lokacin da ya kawo wajen Jiƙamshi
sai ya tsaya sannan ya aje kekensa) Sannunka da hutawa, ko ka ga wasu ɗalibai
nan suna shawagi? Mun fito ran gadi ne domin tafiya da ɗalibai
marar sa zuwa makaranta.
Jiƙamshi Yanzu kuwa na ke shirin tashi in
kai ƙarar
Mai-rogo wajen Hedimasta, kullum sai ya tare ‘yar gidan Malam Ɗanliti
a cikin gidansa in matarsa bata nan.
Malami na ɗaya (Ya zazzaro ido) kar dai in ce ‘Yar auta?
Jiƙamshi: Ina
tsammani ita ce.
Malami na ɗaya Yanzu ina Mai-rogo?
Jiƙamshi Ya shiga cikin gidansa, (ya xan
yi qasa-qasa da murya sannan) itama ‘yar autar tana cikin gidan.
Kafin Malam ya
shiga gidan Mai-rogo sai ya tafi caji ofis da ke kusa da su, ya tafo da
‘yansanda guda uku, aka zo aka kama Mai-rogo hannu dumu-dumu, sannan aka tafi
da shi. Bayan da aka gama tuhumarsa, aka kai shi kotu sannan alƙali
ya yanke masa hukunci. Ita kuwa Talatu ta yi nadama, daga ranar bata ƙara ɗaurawa
‘ya’yanta talla ba.
Abin da Wasan Ƙwaiƙwayon Yake Koyarwa
·
A guji yin talla marar amfani.
·
A bar fifita neman kuɗi bisa neman ilimi.
·
Ɗalibai
a guji guduwa daga makaranta.
·
Idan iyaye sun tura ku makaranta, a
tafi.
·
Ɗalibai
a guji shiga gida idan wani ya kira ku.
·
Kar a laɓe ko a tafi gidan ƙawaye ko wankan tafki ko yawo
marar dalili.
Tambayoyi
1.
Mene ne jigon wannan
labari mai suna ‘Matsalarmu a Yau’?
2.
Lissafa sunayen ‘yan
wasa guda biyar a cikin labarin?
3.
Ware manyan ‘yan wasa.
4.
Ware ƙananan
‘yan wasa.
5.
Cikin layi biyu,
bayyana halin Malam Ɗanliti.
6.
Cikin layi biyu,
bayyana halin Talatu.
7.
Cikin layi biyu,
bayyana halin Jiƙamshi.
8.
0 Comments