C1.2 Wasannin
Dandali
Ɗalibai su ba da bayanin wasannin dandali, su
tantance wasannin dandali sannan su fito da fa’idojin wasannin dandali. A yi
amfani da hotuna da talabijin da bidiyo da kaset da litattafai da dandali wajen
koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.
Bayanin Wassanin
Dandali
Wasan dandali wasa ne da ake gada iyaye da kakanni domin
nishadi da kuma fadakar da juna dangane da yadda rayuwar yau da gobe ke tafiya
a cikin al’umma. Irin wannan wasa ana gudanar da shi a dandali, inda mutane
maza da mata, yara da manya ke zagaye ‘yan wasa domin su yi kallo. Ga wasu daga
cikin misalan wasannin dandali:
1. Wasan ɗan akuyana
2. Tafa-tafa
3. Carmangade
4. Asha ruwan tsuntsaye
5. Tsalle-tsalle
Bayanin
Wasannin Dandali
Ga bayanin yadda ake gudanar da
wasu daga cikin wasannin dandali:
Wasan Shaɗi
Ana yin wannan wasan shaɗi a dandali inda maza da
mata, yara da manya kan zagaye ‘yan wasa domin kallon yadda ake gudanar da
wasa.
Wasan shaɗi yana ɗaya daga cikin bukukuwan Ƙasar Hausa. Wasa ne da
Fulani ke yin sa. Babbar manufar wannan wasa ita ce nuna jarumtaka. Fulani suna
ganin saurayin da bai yi shaɗi ba a matsayin rago.
Ana yin shaɗi ne ta hanyar duka da bulalar da sai dabbobi kamar jakai da
makamantansu za a iya duka da ita su zauna lafiya. Matashi Bafulatani zai cire
rigarsa, sai ya zauna ko a kan turmi, ko ya dogara ƙafa ɗaya
a kan wani, da makamantansu. Sai abokin shaɗinsa ya samo bulala itacen
tsamiya ya riƙa buga masa, shi kuma yana tsaye. Idan ya jure wannan bulala zuwa
adadin da ya ɗauka; wasu sukan ɗauki biyu har zuwa goma sha biyu, wasu ma har fiye, to sukan samu
kwarjini a wajen maza sannan kuma su samu farin jini a wajen mata fulani
'yan'uwansu.
Wasan Dambe
Ana yin wannan wasan dambe a dandali inda maza da mata, yara da
manya kan zagaye ‘yan wasa domin kallon yadda ake gudanar da wasa.
Dambe wasa ne na gargajiya da ake yi a Ƙasar Hausa. Mahauta
su suka keɓanta da wannan wasa na dambe. Ana yin wannan wasa ne domin nuna
jarumtaka. Duk saurayin da bai yi dambe ba, mahauta ‘yan’uwansa suna kallonsa a
matsayin rago, har takan kai ma ga matar aure ta yi masa wahala.
Ana yin wannan wasa ne na dambe ta hanyar bugun juna da naushi da
kuma harbi da ƙafa. An fi yin wannan wasa a lokutan kaka wato ƙarshen
damina. Duk wanda aka nusa ya kai ƙasa to an yi kisa kenan wato
an kai wani ƙasa.
Wasan Kokowa
Ana yin wannan wasan kokowa a dandali inda maza da mata, yara da manya
kan zagaye ‘yan wasa domin kallon yadda ake gudanar da wasa.
Kokawa wasa ne da ake yi a Ƙasar Hausa, musamman
a lokutan kaka. Manoma su suka fi yin wannan wasa. Suna da makaɗansu
na musamman. Daga cikin makaɗan maza akwai masu kiɗan kokawa.
Ana gudanar da wannan wasa ne a zamanin baya domin nuna ƙarfi
da fasaha ko dabara. Saurayin da ke jin ƙarfinsa ya kai, ko
wayonsa ya kai, sai ya yi ɗamara ya tafi fagen kokawa ya je ya tari daidai da shi, su yi ta
bugawa har sai an samu wanda ya kada wani.
0 Comments