Gabatar Da Rubutun Wasiƙa
A koyar da xalibai yadda ake fara rubuta wasiƙa, su tantance yadda ake rubutun wasiƙa, xalibai su
san ma’anar wasiƙa sannan su bada misalin rubutun wasiƙa, a jagoranci xalibai su cike gurabun dake cikin
wasiƙa. A yi masu
tambayoyi sannan a tabbatar sun bayar da amsoshi. A yi amfani da litattafai da
katuttuka da samfurin wasiƙa.
Ma’anar Wasiƙa
Wasiƙa
na nufin rubutaccen saƙo ko bugagge wanda ake sakawa cikin
ambulan sannan a aika saƙo ga wani mutum ko ƙungiya ko hukuma da
sauransu.
Muhimmancin Wasiƙa
· Ana rubuta wasiƙa don aikawa da gaisuwa ko wani saƙo
na musamman.
· Ana sanar da labarai ga waxansu mutane da ke nesa ta hanyar
wasiƙa.
· Ana rubuta wasiƙa don ƙulla
cinikayya ko wata harkar kasuwanci.
· Saƙon wasiƙa yafi na baki inganci saboda shi
babu ƙari ko ragi a cikinsa.
Muhimman Abubuwa Wajen Rubuta Wasiƙa
Muhimman abubuwan da ya kamata a
sani kafin rubuta wasiƙa su ne
kamar haka;
Adireshi:
Adireshi yana ƙunshe da lambar gida da sunan layi da sunan
unguwa da lambar akwatin gidan waya, da sunan ƙaramar
hukuma sai sunan jiha, daga ƙarshe sai
a saka kwanan wata. Haka kuma, ana rubuta adireshi ne a hannun dama na takardar
da aka rubuta wasiƙa a
samanta.
Gaisuwa/Gabatarwa: Gabatarwa
ita ce farko a cikin wasiƙa, bayan
an rubuta adireshi, ana farawa da gaisuwa a cikin wasiƙa sannan
gabatar da kai.
Gangar
Jiki: Gangar
Jikin wasiƙa ita ce inda mai rubutu zai yi bayanin
dalilin da yasa aka rubuta wasiƙa da kuma
ra’ayinsa da buƙatarsa.
Rufewa: rufewa
ita ce a ƙarshen wasiƙa, ana
rufewa ne da sallama.
Misalin Wasiƙa:
Wasiƙar da Malam
Bello ya tura wa xansa mai suna Abdallah:
Jimlolin da za ayi amfani da su:
Fatan alƙairi.
Gaisuwa mai
tarin.
Kimiyya da
Fasaha.
Ilimin sanin
xan’adam.
Rubuto maka
wannan wasiƙa.
Iissafi da
kimiyya da Ilimin tsirai da dabbobi.
0 Comments