Talla

A3.1 Ci gaba Da Rubutun Wasiƙa

 

Ɗalibai su rubuta wasiƙa ga iyayensu da yan’uwansu da abokana riziƙinsu. A yi amfani da litattafai da talabijin da rediyo da hotuna da katuttuka wajen koyar da ɗalibai. Ɗalibai su amsa tambayoyi a ƙarshen darasi.

Bayanin Wasiƙar Iyaye Da Yan’uwa Da Abokan Ariziƙi

Wasiƙa saƙo ne da ake turawa wa wani ta hanyar rubutawa a cikin takarda, a kan rubuta wasiƙa zuwa ga iyaye ko yan’uwa ko abokan arziƙi. Wasiƙar da ake rubuta wa iyaye ko yan’uwa ko abokan arƙiki ba iri ɗaya take da wasiƙar da ake rubuta wa abokai ba. Tana da siga da dubaru da kuma yadda ake rubuta ta.

A cikin wasiƙar a kan yi gaisuwa ta girmamawa da nuna ban girma da sallamawa da kuma nuna halin ɗa’a da biyayya ga wanda aka rubutamawa, haka kuma a kan rubuta wasiƙar sikin salo da dubaru da zaɓar kalmomi waɗanda suka dace da wanda aka rubutamawa.

Ga misalin wasiƙa zuwa da iyaye:          

                               Gida mai Lamba 1,

                               Tudun Mai Sallah,

                               Kaduna, Jihar Kaduna.

                               2 ga watan Janairu, 2020

     Zuwa ga maihaifina,

    Bayan dubun gaisuwa mai tarin yawa, da neman albarka da ɗaukaka daga gareka, da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya da aminci da ɗaukaka daga Allah mabuwayin halitta, maɗaukakin Sarki, Allah ya sa haka amin summa amin.

      Bayan haka, ɗalilin da yasa na rubuto maka wannan wasiƙa, domin in gaida ka, sannan kuma in nemi albarka tare da roƙo a gareka. Baba kamar yadda aka saba taimakonmu tun daga yarintar mu har zuwa girmanmu, yanzu ma ina roƙo a taimaka mani da sayen wasu litattafai waɗanda za su taimaka mani wajen karatuna.

      Kamar yadda ka sani, yanzu muna aji shidda ne, muna shirin zana jarabawar da zata kai mu aji ɗaya na gaba da sakandare. Don haka, muna buƙatar ƙara maida hankali.

    Bisa wannan roƙo da nake yi maka, ina so a saya mani litattafan lissafi na aji shidda da na turanchi da na kimiyya da na Hausa da kuma littafin koyon Komfuta, haka kuma in za a saya mani, to a sayi wanda kamfanin Educate Series suka yi ɗab’in saboda suna yin ingantaccen bugu, suna kuma bin hanyoyin da ɗalibai za su fahimci darasi cikin sauki a cikin litattafansu.

    Daga ƙarshe ina roƙo, a tanadar mani wasu ‘yan kudaɗe waɗanda zan riƙe idan na tashi zuwa zana jarabawa. Ina maka fatan alhairi duniya da lahira.

 

                               Daga ɗanka,

                               Muhammadu Bello

Misalin wasiƙa zuwa ga yan’uwa:

                          Lamba ta 22,

                          Unguwar Fulani,

                          Katsina, Jihar Katsina.

                          2 ga watan ogusta, 2020

     Zuwa ga ɗan’uwana,

   Bayan gaisuwa irin ta addinin musulumci, da nuna ƙauna da yarda da zumunci da aminci a gare ka, da fatan kai da sauran yanuwana kuna cikin ƙoshin lafiya.

     Bayan haka, abin da yasa na rubuto maka wannan wasiƙa, shi ne, domin in jadadda zumuncina a gareka, sannan kuma in yi maka albishir na cewa na kusa kamala makarantar firamare, kuma ina fata in fita da sakamako mai kyau yadda zan samu makarantar koyon kimiyya da fasaha irin wadda ka ke yi.

     Kuma ina farin cikin sanar da kai cewa, yanzu haka baba ya saya mani litattafai waɗanda za su taimaka mani wajen koyon lissafi da turanci da kimiyya da Hausa, wani shahararen kamfani mai suna Educate Series ne ya wallafa litattafan kuma suna da inganci sosai.

     Daga ƙarshe ina ƙara jadadda ƙaunata da zumunci a gare ka, don Allah ka gaida mani sauran yanuwa da abokan arziƙi da aminaina. Ina maka fatan alkairi duniya da lahira.                           

 

                                     Daga ɗan uwanka,

                                     Abdallah Bello

Misalin wasiƙa zuwa ga abokin arziƙi:

                                                                            

                        Lamfa 33,

                        Rumbun kuɗi,

                        Kano, Jihar Kano.

                        2 ga watan Afrilu, 2020

 

     Zuwa ga aminina Bello,

     Bayan gaisuwa mai yawa, da fatan kana cikin ƙoshin lafiya. Ya su baba da baba da sauran ƙanaina na gidanku? To a gaida mani su.

     Kwana biyu ba mu sada zumunci ba, gashi ina ta so in zo domin mu tattauna wata shawara da kai, kasan kwana biyu bana gari, baba ya turani wani aiki da zan kular masa da shi. Tun bayan kamala makarantar firamare sai ya tura ni domin kar in zauna haka nan babu wani abu, kafin jarabawarmu ta fito.

     Shawarar da nake so mu yi aminina ita ce, game da babur da nake so baba ya saya mani, to ya ce in dai na samu sakamako mai kyau zai sai mani keke, maimakon babur. To amma dai ni nafi son babur, don haka ya ka ke ganin zan tuntuɓe shi da maganar sayen babur ɗin?

     Haka kuma, ina so ya samar mani makarantar kimiyya da fasaha, bisa wannan kuwa na tabbatar zai samar mani, saboda shima yana so in zama cikakken injiniya ko injiniyan zane-zanen gidaje.

     Daga ƙarshe ina maka fatan alƙairi, Allah ya ƙara danƙon zumunci a tsakaninmu, sai na ga sakon amsata.

 

               Daga abokin arziƙinka,

               Abbas Bello

Yadda ake rubuta wasiƙa

Waɗancan misalai na wasiƙu da suka biyo baya, in aka lura, an rubuta wasiƙar ne da sigogi ta hanyar amfani da adireshi, gaisuwa, gundarin jawabi, rufewa sai kuma sunan wanda ya rubuta wasiƙar.

Ga abubuwan da ya kamata a koya, yadda ake rubuta su a cikin wasiƙa:

  1. Adireshi
  2. Gaisuwa
  3.  Gundarin jawabi
  4.  Rufewa
  5.  Sunan wanda ya rubuta wasiƙa.

 Aikin Aji

  1. Rubuta wasiƙa ga iyaye ko ‘yan’uwa ko abokan arziƙi, a yi cikakken bayanin dalilin da ya aka rubuta wasiƙar.

                                                               

 

  

             

Post a Comment

0 Comments