Talla

A3.1 Ci Gaba Da Rubutun Hannu

 

Ɗalibai su iya rubuta baƙaƙe da wasula, su bayyana abin da aka faɗa masu ta hanyar rubutu da hannunsu. A yi amfani da fensiri da littafi. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

Rubuta bayanai

A rubuta misalin bayani a saman allo, ga misalin wani bayani:

Bayanin Tsuntsu Mai Tafiyar Dogon Zango

Tsuntsu mai doguwar jela ya tashi daga Alaska da ke Amurka, inda ya sauka a New Zealand, bayan shafe kwanaki 11 yana tafiya ba tare da yada zango ba, wannan tsuntsu ya shiga cikin tarihin tsuntsaye masu tafiyar dogon zango, kuma shi ne kalar tsuntsu na farko da ya yi irin wannan tafiya.

Masana kimiyyar sun ce sun riƙa bin sawunsa ta hanyar wata na'urar bibiya ta zamani. Sun ƙara da cewa tsuntsaye nau'ukan wanda ya nuna wannan bajinta a yanzu, ba sa bacci yayin da suke tafiya, hasalima sukan iya tsamurewa don rage girman jikinsu ta yadda za su yi doguwar tafiya ba tare da wata gajiya ba.


Zubin hallitar irin wannan tsuntsu tamkar kirar jirgin yaƙi ne. suna da dogayen fukafukai da ke taimaka masu wajen yin tashi tamkar jirgi. Tsuntsun wanda jinsin namiji ne da ke da launin shuɗi da ja da kuma fararen zobuna da aka maƙala masa a ƙafafunsa, an kuma maƙala masa wani ɗan ƙaramin tauraron ɗan adam mai nauyin giram biyar a ƙasan bayansa, don bai wa masana kimiyyar damar bibiyar halin da yake ciki. Yana ɗaya daga cikin huɗun da za su bar cikin laka a Alaska, inda a can ne suke rayuwa suna tsintar tsutsa da tanar da suka kasance abincinsu tsawon wata biyu.

Bayanin Yadda Wani Ɓera Ya Samu Lambar Yabo
An ba wani ɓera lambar yabo saboda gano bama-bamai, wannan ɓera ya shigaa kundin tarihi. Beran mai suna Magawa ya sansano nakiyoyi 39 da abubuwan fashewa 28 a tsawon rayuwarsa ta aiki.
Kungiyar liktotin dabbobi ta Birtaniya ta mika wa ɓeran lambar yabo ta zinare saboda kare rayukan jama'a da ya yi lokacin yana aiki, da kuma kawar da ɓaraguzan da aka binne nakiyoyi da ka iya fashewa.


A cikin dabbobi 30 da aka bai wa lambar yabon, Magawa ne ɓera na farko. Wata kungiya ce ta horas da beran mai shekara bakwai, wanda dan asalin kasar Tanzaniya ne.
Magawa yana iya zagaye fili irin wanda ake buga kwallon tennis cikin minti 20, hakan na iya daukar mutum mai rike da na'urar gano bama-bamai ko abubuwan fashewa tsakanin kwana daya zuwa kwana hudu.
Wannan ɓera dai yana ɗaya daga cikin dabbobin da suka samu lambar yabo a shekarar 2020 a faɗin duniya, ya nuna tsananin jajircewa da nuna fasaha irin ta dabbobi.
 Bayanin Kimiyya

Kimiyya wani ilimi ne da yake nazartar abubuwan dabi'a da suke kewaye da mu. Ilimin ya dogara kan wasu matakan gano hakikar abubuwa ta hanyar gwaje-gwaje da ake kira. Masana kimiyya na lura da yadda dabi'a ke tafiya a sararin duniya ta hanyar lura, ɗanɗano, ji, gani ko shinshina. Dakin da ake gwaje-gwajen kimiyya shi ake kira da "laboratory" a turance. Kimiyya ta rabu gidaje daban-daban amma tushensu ya hada da ilimin rayuwa da ake kira da Biology, ilimin Fiziks da kuma ilimin Kemistare. Akwai ilimai da yawa da suka fita daga karkashin Kimiyya kamar na sararin subhna da ake kira da "Cosmology", na taurari da ake kira da "Astronomy", na kananun abubuwa da ake kira da "Ƙuantum Mechanics", da dai sauransu da yawa.

Akwai kuma wasu iliman da suke danganta kansu da kimiyya saboda suna kwatanta yadda kimiyyar ke aiki a tsarin bincikensu. Irin wadannan ilimai sun hadu a bangaren da ake kira Kimiyyar Jama'a (Social Science) kamar ilimin tattalin arziki (Economics), Kimiyyar siyasa (Political Science) da kuma ilimin halayyar jama'a (Sociology). Wadannan ilimai ana kiransu da Kimiyya ne saboda suna kokarin nazartar rayuwar dan Adam ko jama'a kuma su fitar da nazariyyoyi da su ke kokarin sharhi na musamman kan dalilin da ya sanya wani abu ke faruwa a cikin jama'a.


Fanni ne na ilmi mai kula da abubuwa kamar ruwaiskadaskararren abu da dai sauran su. Kimiya na sarrafa wadannan abubuwan dan kera wadansu. Duk abubuwan da muke amfani da su, kamar lantarki, roba, mai, takalmi, Mota, keke, jirgi duk ana sarrafasu ne daga kimiya. Wato kimiyya fanni ne na sani wanda ya shafi garwaye garwaye na abubuwa ingattatu. 

Aikin Aji
  1. Yi taƙaitaccen bayani a kan Kimiyya.
  2. Rubuta bayanin tsuntsu mai tafiyar dogon zango a cikin littafi mai jan layi.

 

 

Post a Comment

0 Comments