Talla

A3.1 Ci Gaba da Ƙa’idojin Rubutu

 

Ci Gaba da Ƙa’idojin Rubutu

Ɗalibai su iya kiyaye ƙa’idojin rubutu, su san yadda akae fara jimla da babban baƙi ko wasali, su san yadda ake amfani da ‘aya’. A tabbatar da cewa, ɗalibai sun iya tantance farkon jimla, sannan su san muhimmancin ‘aya’. A yi amfani da litattafai da ƙasidu da jaridu da katuttuka wajen koyar da ɗalibai.

Ma’anar Ƙa’idoji Rubutu

A darussan da suka gabata, an bayyana cewa ƙa’idojin rubutu dokoki ne da ake bi a jeranta kalmomi, tare da bin salo da ƙa’idoji ta yadda za a samu ingantacciyar jimla mai ma’ana. A cikin dokoki ko ƙa’idojin rubutu akwai alamomi da ake amfani da su wajen rubutu, da su ne ake yin ishara wajen tsayawa da magana ko nisawa ko tambaya ko ishara ko nuni da wani abu. Waɗannan ƙa’idoji ko alamomin magana suna taimaka sosai wajen isar da saƙo sannan kuma a gane abinda aka rubuta. Ɗalibai na nuna kwarewarsu a fagen rubutu ne kawai idan sun yi hazaƙa sun koyi yadda ake rubutu da ingantacciyar Hausa da yin amfani da ƙa’idojin rubutu a cikin rubutunsu.

Tantance Farkon Jimla

In aka ce jimla, ana nufin jeranta kalmomi don a samar da cikakkiyar gaɓar mai ma’ana. Kalmomi da jimloli suna wakiltar furuci da maganar da ake yi, don haka ana rubuta jimla ne ta hanyar ƙa’idojin rubutu domin a samar da gaɓar magana ko jimla mai cikakkiyar ma’ana.

Kowace jimla tana farawa da babban baƙi. A darasin da ya gabata can baya, an bayyana cewa akwai: jimlar bayani, jimlar umurni da jimlar tambaya, duk jimlar da za a rubutu, kodai ta bayani ce watau mai bayyana wani abu, ko ta tambaya ce ko ta umurni ce, ana fara rubuta ta da babban baƙi.

Ga misalai:

Jimlar Bayani:

Bello yana rubutu da kwamfuta.

Kwamfutar Bello ta lalace.

Abdallah ya sawo wa babansa wata sabuwar Kwamfuta.

Muhammad ya raka babansa kasuwa don su gyara Kwamfuta.

 Idan ɗalibai sun lura, waɗancan jimloli da aka rubuta, suna yin ƙarin bayani ne a kan Bello da Kwamfutarsa, dukkan jimlolin an fara rubuta su da babban harafi, watau kalmar farko a cikin jimlar, harafin farko na kalmar an rubuta shi da babban baƙi ko babban wasali. In aka lura haruffan da aka rubuta da babban baƙi sannan aka ja masu layi su ne haruffa na farkon jimla.

Jimlar Umurni:

Ɗauko litattafan.

Zauna ka yi rubutu.

In ka gama rubutu, ka yi karatu.

Yi tilawar abinda ka karanta a cikin aji.


Idan ɗalibai sun lura, waɗancan jimloli da aka rubuta, suna yin umurni ne ga wani, dukkan jimlolin an fara rubuta su da babban harafi, watau kalmar farko a cikin jimlar, harafin farko na kalmar an rubuta shi da babban baƙi ko babban wasali. In aka lura haruffan da aka rubuta da babban baƙi sannan aka ja masu layi su ne haruffa na farkon jimla.

Jimlar tambaya:

Ya sunanka?

Ina zaka je?

Ka je makaranta yau?

Ka yi karatu a makaranta?

 Idan ɗalibai sun lura, waɗancan jimloli da aka rubuta, suna yi wa wani tambaya ne, dukkan jimlolin an fara rubuta su da babban harafi, watau kalmar farko a cikin jimlar, harafin farko na kalmar an rubuta shi da babban baƙi ko babban wasali. In aka lura haruffan da aka rubuta da babban baƙi sannan aka ja masu layi su ne haruffa na farkon jimla

Muhimmancin Aya

In aka ce ‘aya’ a cikin rubutu ana nufin alamar tsayawa a ƙarshen cikakkiyar jimla. Ana ɗasa alamar ‘aya’ idan rubutu ya cika, don a nuna cewa ƙarshen jimla ta ƙare. Alamar ‘aya’ ita ce kamar haka: (.) wato ɗigon da aka rubuta cikin baka biyu.

 ·               Ana amfani da alamar ‘aya’ a muhimman wurare kamar haka:

·               Don a tabbatar da cikar jimla.

·               Don a nuna cewa magana ta ƙare.

·               Don a fidda cikakkiyar ma’ana a ƙarshen jimla.

·               Don a samu damar ci gaba da rubuta wata jimlar, inda ake tashi da babban baƙi a jimla ta gaba bayan an ɗasa alamar aya.

Wuraren da Ake Amfani da Alamar Aya

Wuraren da ake amfani da alamar aya su ne kamar haka:

Ana amfani da alamar aya a cikakkiyar jimlar Hausa mai ɗauke da cikakkiyar ma’ana.

Ga misalin jimloli da yadda ake ɗasa alamar aya a ƙarshensu:

·        Yaro yana tuƙa keke.

·        Ade tana dama fura a cikin kwarya.

·        Ashiru ya hau dokinsa danda.

 Ana amfani da alamar aya domin a raba jimla da wata jimla, wato don a nuna cewa jimlar farko ta zo ƙarshe, sannan kuma a tashi da wata sabuwar jimlar, duk jimlar da aka tashi da ita ana fara rubuta ta da babban baƙi.

Ga misalin ƙarshen jimla da yadda ake ɗasa alamar aya sannan a tashi da babban baƙi:

·        Wannan rahama ce da ga Allah maɗaukaki. Sai ka gode masa.

·        Rabon kwaɗo baya hawa sama. yanzu ya samu arziƙin zaman duniya.

·        Idan aka daka taka, an sha wahala. Ka bi ra’ayin sarki ka zauna lafiya.

 Ana amfani da alamar aya a tsakanin haruffan da aka rubuta don a taƙaita sunan wani, ko wani kamfani ko wata ƙungiya.

Ga misalin alamar aya a tsakanin haruffan da aka taƙaita:

 ·        Jami’ar U.M.Y.U.K, a nan haruffan da aka taƙaita suna nufin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina.

·        Kwalejin F.C.E Katsina, a nan haruffan da aka taƙaita suna nufin Makarantar Horar da malamai ta FCE, Katsina.

·        D.r, waɗannan haruffa da aka taƙaita suna nufin Dakta.

 Ana amfani da alamar aya domin a rubuta adireshin shafin intanet, ga misalai:

 

www.arewanews.org.ng

www.arewanewsng.com

www.litattafai.com

www.abc24radio.com

www.belloida.com

www.melon.com

 Idan ɗalibai sun lura, duk waɗancan adireshin da aka rubuta na intanet, a saƙa alamar aya a tsakanin haruffan domin a bambance ɓangarorin adireshin.

 Tambayoyi

1.     Kawo rabe-raben jimla guda uku?

2.     Me ake nufi da ƙa’idojin rubutu a Hausa?

3.     Kawo muhimmancin alamar aya guda uku?

4.     Waɗanne wurare ne ake amfani da alamar aya?


 

Post a Comment

0 Comments