Talla

A2.1 Karatu Don Auna Fahimta

Karatu Don Auna Fahimta

A jagoranci ɗalibai su karanta waɗannan labarai da ke biye da kansu, sannan a basu dama su bayar da labari na kansu ko su kawo labarin da suka karanta tare da ma’anar muhimman kalmomi a cikin labaran. A basu dama su karanta labaran a bayyane da kuma cikin zuci. Ɗalibai su amsa tambayoyi, ayi amfani da litattafai da ƙasidu da talabijin da rediyo da faifan CD da katuttuka wajen koyar da ɗalibai.

Ci Gaban Labarin:

Karambana Ko Ka Ga Dokin Sarki Na Biyu

Daidai lokacin da zai fita daga gidan Sarki sai ya ci karo da Karambani ya sato dokin gimbiya watau danda, shi ma fadawa sun biyo shi daga turken dokin a sukwane. Yana zuwa daidai inda Karambana ya ke, sai ya miƙo masa hannu, shi kuma ya kama ya haye bisa dokin, suka sukani doki sai bayan gari, fadawa suka rufa masu baya, amma suna ficewa ta ƙofar ‘Yanɗaka sai suka shafi layoyi suka bace.

Shi kuwa Malam yana ganin duk abinda su Karambana su ka yi ta wani madubin sihirinsa, ya tabbata sarki sai ya turo fadawa don su tafi da ‘ya’yansa, ya kai su kurkuku bisa laifin da suka aikata. Daga bisani a kai su makarantar boko, shi kuwa babu abun da ya tsana a rayuwarsa face turawa da makarantarsu. Don haka sai Malam ya shiga ɗakin sihirinsa ya kulle, a cikin ɗakin kuwa akwai kayan sihiri da wata ƙatuwar tukunya wacce ke ci da wuta koda yaushe, sannan kuma akwai kayan da yake haɗa sihirinsa da su irinsu; banten baƙin biri, kitsen zaki, fatar damisa, toron giwa, haƙoran kura da gemun dila.

Lokacin da farin hayaƙin jakar ƙudiri ya zuƙe Karambani da Karambana sai ya furzar da su can ƙasar Zazzau, iyaka da ƙasar Katsina.

Karambana ya kalli Karambani sannan ya ce masa,

“Kaga inda Allah ya kawo mu?”

Karambani ya ce,

“Na so ace ka sato gimbiya mun tafo yawon buɗe ido tare”

Karambana ya ce,

“Ni kuwa na so ace da Danda muka taho, da mun samu abun hawa”

Daga nan sai suka shiga cikin daji har suka isa wata gona ta wani bazazzage, ƙabilun da ke yankin Hausa da Fulani ne amma akwai Gwari sannan kuma akwai wasu ƙabilu a yankin, mafi yawan ƙabilun manoma ne.

Su ka ɗan ratsa kaɗan sannan suka shiga wani lambu inda ake noman rake da lemu da gwanda da abarba. Wani ɓangare na gonar kuma ana noman doya da rogo da dankali da agushi.

Karambana ya yanko itatuwan rake da lemu da gwanda da abarba sannan ya tara gefe ɗaya. Shi kuwa Karambani ya yanko itatuwan doya da rogo da dankali da agushi shi ma ya tara gefe ɗaya. bayan sun ci sun ƙoshi sai suka ƙura wa itatuwan idanu suna son gane bambancin itattuwan.

Karambana ya ɗanɗana zaƙin kowane daga cikinsu, sannan ya ce,

“Ko ka san yadda ɗanɗanon waɗannan ‘ya'yan itatuwa ya ke?”

Karambani ya girgiza kai alamar a'a, sai Karambana ya ci gaba da bayyana masa abinda ya fahimta game da bambancin ɗanɗanon itatuwan ya ce,

“Tsirai sun ƙunshi abinci me sukari da mai sannan kuma akwai tsirai da ke da sitaci, ana matse sikari daga karan rake, sannan a matse mai daga kwayar gwaɗa, ana matse ruwan rogo don a samu sitaci”

Daga nan sai Karambana ya saka hannayensa a cikin jakar ƙudiri sannan ya kudurta yana son wuƙa da ƙyalle da baho da dutsen niƙa da ruwa, take sai waɗannan abubuwa suka faɗo, sannan ya ɗauka.

Ya yanki rogo, sannan ya ɓare fatar ya sanya ruwa ya wanke shi, ya niƙa rogon sannan ya zuba rogon cikin ƙyalle wanda ya tarba saman bahon, ya zuba ruwa sannan ya matse, sai ga ruwan sitaci na zuba a cikin baho. Bayan ruwan sitacin ya gama taruwa sai ya shanya shi can gefe ɗaya.

Karambana ya kalli ɗan ‘uwansa ya ce,

“Ka ga yadda ake yin sitaci”.

Muhimman Kalmomi

Kalmomi

Ma’anarsu

Bacilmi

Namijin barewa

Ragon daji

Rago ne na daji mai ƙahonni da yawa.

Ƙwaron luna

Ƙwaro ne da ke rayuwa a cikin daji.

Karkanda

Dabba ce mai ƙaho a saman goshi, tana da girma da ƙarfi.

Yanyawa

Dabbar daji ce.

Giwar ruwa

Dabbace mai girma da ke rayuwa a cikin ruwa.

Ƙudan tsirya

Ƙuda ne da ke rayuwa a cikin daji, yana da girma fiye da ƙudan gida.

Tsutsar katafila

Tsutsa ce da ke rikiɗa da zama wani ƙwaro.

Tsutsar silika

Tsutsa ce mai salƙi da ake samu bisa ita ce.

Mangus

Wata dabba ce da ke rayuwa a cikin daji tana cin nama, tana kama da kare amma ba ta kai kare girma ba.

Ƙuduri

Aniya, buƙata, buri dake cikin zuciya.

Furza

Fesar da ruwa ko iska ko wani abu.

Budari

Dabbar daji ce mai yawan sakin iska.

Kamuku

Daji ne dake cikin ƙasar Zazzau.

Falgore

Daji ne da ke cikin ƙasar Kano.

Shawagi

Yin tafiya da fukafukai a sararin samaniya.

Yassare

Yin kyautar baiwa daga Allah.

Aikin Aji:

1.     ɓi daga cikin kalmomi ka cike guraben da ke biye a gutsiren labarin da za a kawo nan gaba:


Labarin Auna Fahimta

Su ka yi ta ______________a cikin ______________da ke ƙasar _____________wanda ya nausa ya haɗe da dajin _____________na ƙasar Kano ya dangane da dajin Yankari na____________. Suna tafiya suna kallon hotunan _____________dangin su; zaki, __________, damisa, barewa, bacilmi, ragon daji, raƙumin daji, karkanda, ____________, Yanyawa, giwar ruwa, ƙudan tsirya, ____________, tsutsar siliki da________________.

Amshoshi

(a) Sarƙe-haƙori             (b) Sarƙar wuya             (c) Sarƙa     

(a) damuwa                   (b) Ake Kamuwa            (c) Ake Kallo

(a) Matsanancin             (b) ciwo                        (c) Fitina

Tsokokin Jiki                  (b) Wuya                       (c) Rai

(a) makaranta               (b) Jiki ta bi Jini             (c) Kasuwa

(a) manya da raya         (b)manya                      (c) yara

(a) hanyar makaranta    (b) Numfashi                 (c) lumfashi

(a) Kimiyya ya gano      (b) kimiya                      (c) fasaha

(a) faɗin gari                 (b) cikin gari                  (c) Faɗin duniya

(a) marar taushi            (b) marar lema              (c) Mai lema



[1] An ciro wannan labari daga littafin ‘Karambana ko kaga Dokin Sarki’ wanda Bello Hamisu Ida ya rubuta a shekarar 2018 wajen kos din bitar kagaggun labarai wanda Pleasant Library haɗin guiwa da Makarantar Malam Bambadiya suka shirya wa wasu haziƙan maruba.

 

Post a Comment

0 Comments