Ɗalibai su
karanta labarai da kansu, su bayar da labarai na kansu, su kawo labarin da suka
karanta, sannan su kawo ma’anar muhimman kalmomin aikin labarin. A yi amfani da
litattafai da talabijin da rediyo da faifan CD da hotuna da katuttuka. A yi wa ɗalibai
tambayoyi daga ƙarshen
darasi.
Karanta Labari a Bayyane
Ɗalibai su karanta
wannan labari a bayyane:
Ci gaban labarin:
Karambana Ko Ka Ga
Dokin Sarki
Karambana ya kalli ɗan ‘uwansa ya ce,
“Ka ga yadda ake yin sitaci”
Shi kuwa karambani sai ya ce,
“Ni kuwa ɗan uwa abinda ke bani mamaki ga karan rake, yadda ake samar da sikari
daga cikinsa irin wanda muka ɗebo gidan maigari, an ce turawa ne suka fansar masa da sukari”
Sai karambana ya ce,
“Babu wani abun mamaki daga cikinsa, bari ka gani”
Sai ya kama hannun ɗan ‘uwansa suka sanya cikin jakar ƙudiri
suka runtse idanuwansu, bayan wani ɗan lokaci suka buɗe, suna buɗe idanuwansu sai Allah ya yassare masu ilimin yadda ake yin rake.
Karambani ya ɗebo karan rake, sannan ya kudurci abun daka, sai ga turmi da taɓarya da baho da kyalle da tukunya sun faɗo daga
cikin jakar, karambani ya ɓaɓalla karan raken sannan ya zuba cikin turmi, ya shiga bugun karan
har sai da ya yi laushi sosai, ya zuba cikin wani baho, ya tace ruwan raken, ya
zuba cikin tukunya.
Ya samo ƙirare, ya kunna wuta, ya ɗora ruwan raken, ya ci gaba
da rusa wuta har sai da ruwan raken ya gama siraci sannan ya shanya dallakin
sikarin a cikin rana har sai da ya daskare. Karambani ya kalli ɗan uwansa ya ce,
“Wannan shi ne dallakin sukari”
Suna cikin wannan wauta sai mai gona ya jiwo ƙaurin wuta, ya zo, da ya ga irin ɓarnar da
su ka yi masa, sai ya ɗauko bindiga harba-ruga, amma kafin ya isa inda suke sai suka haɗa hannayensu, suka saka cikin jakar ƙudiri,suka
kudurta buƙatarsu watau suna so su koma tsuntsaye. Sannu a hankali suka rikiɗe suka koma maiki da mikiya. Suka yi sama fir! Suka bar mai gona
yana mamakin irin hatsabibancin waɗannan yara da suka yi masa ɓarna.
Su ka yi ta shawagi a cikin dajin kamuku da ke ƙasar zazzau wanda ya nausa ya haɗe da
dajin falgore na ƙasar kano ya dangane da dajin yankari na ƙasar bauchi.
Suna tafiya suna kallon hotunan namun daji dangin su; zaki, kura, damisa,
barewa, bacilmi, ragon daji, raƙumin daji, karkanda, macizai, yanyawa, giwar ruwa, ƙudan tsirya, tsutsar katafila, tsutsar siliki da kwaron luna.
Maiki ya ce da mikiya,
“Shin kin fahimci cewa, dabbobin sun kasu kashi biyu?”
Mikiya ta ce,
“Eh, na lura wasu dabbobin na rayuwa cikin daji wasu kuma na rayuwa
cikin ruwa, wasu jikinsu rufe ya ke da kwasfa, ya yin da wasu jikinsu ke rufe
da firkaki wasu kuma gashi ya rufe jikinsu”
Sai maiki ya ƙara da cewa,
“Akwai dabbobi masu ƙashin baya ɗaya kamar; maciji, kifi, ƙadangare da kada”
Bayan ya yi shiru sai mikiya ta ce,
“Haka kuma akwai masu tafiya da ƙafafuwa
huɗu wasu kuma jan ciki suke yi, ya yin da wasu ke tashi sama”.
Maiki ya ce,
“Ai in aka lura ma cimakar dabbobin ta bambanta, barewa, giwa, ɓeraye, fari, budari duk suna cin tsirrai ne”
Sai mikiya ta ce,
“Amma zaki, kura, damisa, maciji, kare, mangus, jemage, kwaɗi da kifi duk suna cin nama ne, waɗannan
dabbobi ai su ake kira da ‘maciya nama’”.
Mikiya ta ɗan yi shiru sannan ta yi fir! Ƙasa,
bayan ta nazarci tabbobin dake dajin yankari sai ta koma sama, sannan ta ce,
“Hallitar dabbobin ma ta bambanta, ƙafafuwa
da haƙoransu an hallice su don su dace da irin abinda suke ci. Haƙoran kura dogaye ne masu kaifi za su iya yaga nama”
Ta haɗiyi yawu sannan ta ce,
“Haƙoran barewa kuwa suna da faɗi yadda za su iya tauna
tsirrai su niƙe su sosai”.
Daga nan maiki a mikiya suka ci gaba da shawagi, sun haɗu da dabar tsuntsaye da daular zuma da fari, maiki ya kama
sarauniyar fara, fadawanta kuwa suka ce da wa aka haɗa mu,
amma kafin su far masu da yaƙi har sun sauka gefen kogi, suka sake yin siddabaru suka rikiɗa suka koma mutane.
Karambani ya yi nitso cikin teku ya kamo sarauniyar kifaye. Suka haɗa hallitun don su ga bambancin yadda fara da kifi suke numfashi.
Karambani ya ɗauko wani katako ya ɗora sarauniyar kifaye sannan ya sanya itace cikin bakinta ya fiddo
da muƙamuƙin kifin, ya yanke su ya bar soson da ke ciki watau ‘gil’ mai ja-ja,
ya haska da tabaron hannu da ya ɗauko cikin jakar ƙudiri, ya ce,
“Sandunan dake cikin (watau ‘gil’) mai ja-ja da sosansa masu alamar
kaifi su ke motsawa ta hanyar shaƙar iska da fitar da shi,
watau shi ne kamar huhun kifi, da shi yake numfashi”.
karambana ya ɗauko sarauniyar fara ya haska cikin bakinta da tabaron hannu sosai
ya ga yadda take numfashi, ya ce,
“Ita fara bata da muƙamuƙai kamar kifi (watau ‘gil’), bata da huhu, iska na shiga cikin wani
kwararo ne zuwa cikin jikinta”
Ana kiran wannan kwararo da karambana ya gani a jikin fara da
sunan‘sifarakul’ sun yi kama da ɗigo-ɗigo da ke jikin fara. Daga nan sai suka yi zanen fara da kifi da
abubuwan da suka gani a jikin wata takarda sannan suka saka cikin jakar ƙudiri suka nausa cikin daji suna bin gefen tekun don ƙara tantance abubuwan da ke rayuwa a cikin daji.
Bayanin Muhimman Kalmomi
Karambana
|
Mutum mai ɗaukar
magana, wanda duk abun da ya gani ba zai bari ba. |
Ɗan uwa |
Wanda ake da zumunci na jinni da
shi. |
Sitaci |
Wani sinadari ne da ake fitarwa
daga nau’in abinci musamman rogo. |
Karan
rake |
Itacen rake wanda ake shukawa a
fadama. |
Sikari
|
Sinadari ne mai zaƙi wanda ake
fitarwa daga sikari. |
Kudurci
|
Raya wani abu a cikin rai. |
Turmi
|
Abu ne da mata ke daka, ana
sassaƙa shi da
itace. |
Taɓarya |
Da shi ake yin daka, ana sassaƙa shi da
itace. |
Baho
|
Mazubi ne, inda ake zuba wani
abu a ciki. |
Kyalle
|
Ragaya da ake samarwa daga
tufafi. |
Tukunya
|
Wadda ake dafa abinci a cikinta. |
Jaka
|
Ana yin ajiye-ajiye a cikinta. |
Ruwan
rake |
Ruwa ne da ake samu daga cikin
itacen rake in an matshe. |
Mikiya |
Nau’in tsuntsu ne watau namijin
maiki. |
Shawagi
|
Yawo ko tafiya a sararin
samaniya. |
Kamuku
|
Daji ne da ke yankin Kaduna. |
Falgore
|
Daji ne da ke yankin Kano. |
Yankari
|
Daji ne da ke yankin Bauchi. |
Bacilmi |
Namijin jimina. |
Ragon
daji |
Dabba ce da ke kama da rago, ana
samunta a cikin daji. |
Mikiya |
Nau’i ne na tsuntsu. |
Raƙumin daji |
Dabba ce da ke kama da raƙumi, ana
samun ta a cikin daji. |
Karkanda |
Nau’in dabbobin daji ce. |
Macizai |
Maciji wanda ke da jiki mai
kyau, yana jan ciki. |
Yanyawa |
Nau’in dabba ce da ke rayuwa a
cikin daji. |
Giwar
ruwa |
Nau’in dabba ce da ke rayuwa a
cikin ruwa. |
Ƙudan tsirya |
Nau’in ƙuda ne. |
Tsutsar
katafila |
Nau’in tsutsa ce. |
Tsutsar
siliki |
Nau’in tsutsa ce. |
Kwaron
luna |
Nau’in kwaro ne. |
Maiki |
Nau’in tsuntsu ne, watau namijin
mikiya. |
Aikin Aji
- Karanta labarin dake sama a bayyane.
- Fitar da kalmomi masu ma’ana a cikin labarin da ku ka karanta.
0 Comments