Talla

A2.1 Gabatar Da Auna Fahimta: Marubuci Bello Hamisu Ida

 

Gabatar Da Auna Fahimta

A karanta bayanai ko labarai waxanda ke da tambayoyi a ƙarshe, sannan daga ƙarshen karatun a yi tambayoyi da suke biye, a kuma umurci xalibai su bayar da amsoshin tambayoyi. A karanta litattafai da bayanai ko ƙasidu ta hanyar yin amfani da litattafai ko katuttuka don xalibai su fahimci darasi.

 

A karanta waxannan bayanai da ke biye don xalibai su saurara su kuma bayar da amsoshin tambayoyin da ke ƙasa:

 

Cutar Gudawa

Cutar gudawa wani nau’i ne da ya ke sawa ayi ta tsugunni tare da yin gudawa mai ruwa-ruwa a kalla sau huxu ko biyar a duk rana. Wasu lokutan in cutar ta yi tsanani, a kan xauki kwana-da-kwanaki ana gudawa wanda ke jawo bushewar jiki saboda ƙarancin ruwa a cikin jiki, wanda hakan ke sanya wa kamanni su canza sannan fata ta tsane, haka kuma fitsari ya ragu kuma a samu ƙaruwar bugun zuciya, daga bisani kuma a kan fita daga hayyaci idan cutar ta yi tsanani. Abinda ke sa kamuwa da cutar shi ne rashin tsaftar abinci ko ruwa ko kuma yaxuwar cutar daga wanda ya kamu.

 


Cutar gudawa ta kasu kashi uku, su ne kamar haka: gudawa mai ruwa-ruwa, gudawa mai jini-jini da gudawa mai daxewa. Gudawa mai ruwa-ruwa na iya kasancewa saboda kamuwa da cutar kwalara. Idan kuwa akwai gudawa mai jini-jini, an fi kiranta da atini.

 

Gudawa ita kadai ba cuta bace amma alamace da take nuna cewa wani abu yana tafiya ba dai-dai ba a jikin xan-adam. Yara ƙanana musamman na goye sun fi manya shiga cikin haxarin kamuwa da gudawa, kuma yara sukan galabaita sosai fiye da manya a duk lokacin da suka yi gudawa musamman ma idan aka yi rashin dace ta zo da amai (hararwa).

 

Hanyoyin kare faruwar gudawa sun hada da: Tsaftar muhalli, ya kamata a tabbatar da tsaftar muhalli, kamar share gida da kewaye a ƙalla sau uku a rana; amfani da abun zuba shara rufaffe domin barin abun zuba shara a bude kan jawo ƙudaje da ƙadangaru a gida, kuma yara sukansa hannuwansu a ciki domin xaukar wani abun su yi wasa da shi; rufe masai da murfi a koda yaushe, nisantar da masai daga gurin dafa abinci, rijiya da sauransu; zubar da kashin yara a masai da zarar sun gama domin barinsa a buxe a cikin gida kan jawo ƙudaje waxanda za su xauki kwayoyin cuta daga kashin su sa a cikin abinci, ko ruwan sha wanda ke jawo gudawa; rufe randa da murfi wanda zai rufe ta, barinta a buxe kan jawo faxawar kwayoyin cuta cikin ruwan. Ga wanda ya kamu da gudawa ya kamata a bashi taimakon gaggawa a gida kafin a kai shi asibiti, ta hanyar bashi ruwan gishiri da sukari akai-akai.

Bincike ya nuna cewa, duk lokacin da aka fara ruwan sama wato faxuwar damina muhalli ya kan gurɓace saboda ruwa, musamman ma wuraren da mutane suke kashi a fili, da kuma inda ake zubar da shara babu xaukar matakin tsaftace wajen sharar da kuma muhalli, waxannan suna taimakawa sosai wajen yaxuwar cutar gudawa.

Tambayoyi:

1.    Me ke jawo cutar gudawa?

2.    Cutar gudawa ta kasu kashi nawa?

3.    Gudawa alama ce ta?

4.    Lissafa matakai biyu na kariya daga cutar gudawa?

5.    Waxanne alamomi ne ke nuna an kamu da gudawa?

6.    Cike waxannan gurabe:

7.    Cutar gudawa wani nau’i ne da ya ke

8.    Gudawa wanda ke jawo bushewar jiki saboda ƙarancin 

9.    Cutar gudawa ta kasu kashi uku, su ne kamar haka:


Zazzaɓin Lassa

Zazzaɓin Lassa wata cuta ce da ta samo asali daga wani gari da ake kira Lassa a Jihar Borno, cutar na yaxuwa ne a duk wani abu da ɓera ya samu kusantarsa, musamman abinci. Alamomin cutar sun haxa da zafin zazzaɓi, ciwon kai, da amai (haraswa). hanyoyi da ake kamuwa da cutar sun haxa da ajiyar kayan abinci ba tare da kulawa da su ba wanda hakan ke bai wa ɓeraye damar lalata abinci.

 

A duk lokacin da mutane suka ajiye abubuwan amfaninsu, akwai buƙatar sake tsaftace su kafin amfani da su don guje wa kamuwa da cutar. Duk lokacin da ɓera ko gafiya suka yi fitsari ko kashi a cikin abinci, kuma aka ci abinci, ko cin naman ɓera da sauran namomin dabbobin daji, to akwai yiwuwar kamuwa da cutar ba tare da ɓata lokaci ba.

 


Kwayar cutar na yaxuwa ne ta hanyar tu'ammali da abinci da kuma kayayyakin amfanin gida da suka gurɓata da fitsari da kashin ɓera ko kuma ta hanyar shafar duk wani ruwa-ruwa daga jikin mutum da ya kamu. Shan garin kwaki ma yana kawo kamuwa da cutar zazzabin Lassa.

A xauki matakin garzayawa zuwa asibiti da zaran sun fara jin wani canji a jikinsu ko dai na ciwon kai da zazzaɓi ko in an ga ƙuraje a cikin jiki. Hukumar ta NCDC da sauran hukumomin lafiya sun kafa kwamitoci dake da wakilai daga hukumar lafiya ta duniya da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan cutar zazzaɓin lassa. Bincike dai ya nuna cewa cutar zazzabin Lassa tafi yawaita a lokacin zafi kuma cutar tayi tsanani ne a Najeriya a shekara ta dubu biyu da sha takwas.

 

Cutar ta kashe mutum kusan sittin a Najeriya inda ta bazu zuwa jihohi goma sha tara da suka ƙunshi na kudu da arewacin ƙasar. Cibiyar takaita yaxuwar cutuka ta ƙasar ta ce, zazzaɓin ta ƙara bazuwa zuwa jihohi irinsu Kaduna da Benue da Kwara da Riɓers.

 

Sauran jihohin da ke fama da cutar sun haxa da Oyo da Ondo da Kogi da Bauchi da Enugu da Nasarawa da Ebonyi da Filato da Taraba da Adamawa da Gombe da Imo da Delta kuma Abuja. Cibiyar ta ce kusan mutum xari uku aka tabbatar suna xauke da cutar. Cutar wadda ɓeraye ke haddasawa na ƙara sanya damuwa a tsakanin hukumomin lafiya na ƙasar.

 

Lassa na da kamanceceniya da cutukan Ebola da Marburg inda take haddasa zazzabi da haraswa idan kuma ya yi tsanani sai maras lafiya ya fara zubar da jini.

 

Tambayoyi:

1.    Daga wane gari aka fara samun cutar Lassa?

2.    Lissafa dalilai uku da ke haddasa cutar Lassa?

3.    A ƙalla, mutum nawa suka mutu sanadiyar cutar Lassa?

4.    Waxanne jahohi cutar Lassa ta fi yaxuwa?

5.    Waxanne jahohi ne cutar Lassa bata yawaita ba?

6.    Cike waxannan guraben:

7.    Cutar na yaxuwa ne a duk wani abu da:

8.    Hukumar ta NCDC da sauran hukumomin lafiya

 


 

Post a Comment

0 Comments