Talla

A1.4 Sauye-Sauyen Kalma

A darussan da suka gabata, ɗalibai sun koyi yadda ake haɗa baƙi da wasali a samar da kalma. Haka kuma ɗalibai sun koyi yadda ake samar da wata kalma daga wata ta hanyar yin ƙari. A jagoranci ɗalibai su koyi yadda ake yi wa kalma ƙari a gaba ko a baya don a samar da wata Kalmar, ayi amfani da kamus na Hausa da litattafai da taswirar kalmomi domin a koyar da yara yadda za su bunƙasa gandun kalmominsu. 

Ma’anar Sauye-Sauyen Kalma

Sauye-sauyen kalma ƙari ne da ake yi wa kalma domin a sauya ta da wata Kalmar yadda za a samu wata sabuwar kalma mai ma’ana daban da Kalmar farko. Irin wannan ƙari a kan yi shi a farkon kalma ko a tsakiyar kalma ko a ƙarshen kalma. Haka kuma, akwai kalmomi kaɗan da akan yi ƙari a farko da ƙarshen kalma don a samu wata sabuwar kalma mai ma’ana daban.

Ƙari A Farkon Kalma

Ƙari a farkon kalma ƙari ne da ake yi wa kalma a farkonta domin a samar da wata kalmar mai sabuwar ma’ana daban da wadda ake da ita. Ga misalan kalmomin da ake yi wa ƙari a farkonsu: 

Kalma

Ƙari

Sabuwar kalma

noma

Ma + nom + i

Manomi

Gyaran mota

Mai + gyaran mota

Mai gyaran mota

Ja

Man + ja

Manja

Gyaɗa

Man + gyaɗa

Mangyaɗa

Ƙwaƙwa

Man + ƙwaƙwa

Manƙwaƙwa

Shanu

Man + shanu

Manshanu

Ɗinki

Ma + ɗinki

Maɗinki

Jema

Ma + jema

Majema

Aski

Ma + aski

Ma’aski

Faci

Mai + faci

Maifaci

 Ƙarin A Tsakiyar Kalma

Ƙari a tsakiyar kalma, ƙari ne da ake yi wa kalma a tsakiyarta domin a samu wata sabuwar kalma mai ma’ana daban da wadda ake da ita. Wannan ƙari ana yinsa ne a tsakiyar kalma. Ga misalin ƙarin da ake yi a tsakiyar kalma:

Kalma

Ƙari

Sabuwar kalma

Rago

Ra + gu + na

Raguna

Turmi

Tur + a + me

Turame

Raƙumi

Raku + m + ma

Raƙumma

Shanu

Shan + a + ye

Shanaye

Tunkiya

Tu + ma + ki

Tumaki

Akuya

Aku + yo + yi

Akuyoyi

Murhu

Mur + a + hu

murahu

Kurma

Kur + a + me

Kurame

Kasko

Kas + a + ke

Kasake


Ƙarin A Ƙarshen Kalma

Ƙari a ƙarshen kalma, ƙari ne da ake yi wa kalma a ƙarshenta domin a samu wata sabuwar kalma mai ma’ana daban da wadda ake da ita. Wannan ƙari ana yinsa ne a ƙarshen kalma. Ga misalin ƙarin da ake yi a ƙarshen kalma:

Kalma

Ƙari

Sabuwar kalma

Kare

Kar + nuka

Karnuka

Hula

Hulu + na

Huluna

Makaranta

Makaran + tu

Makarantu

Littafi

Litatta + fai

Litattafai

Kujera

Kuje + ru

Kujeru

Kwamfuta

Kwamfu + toci

Kwamfutoci

Mota

Moto + ci

Motoci

Waya

Wayo + yi

Wayoyi

Mashin

Mashi + na

Mashina

Riga

Rigu + na

Riguna

Ƙari A Farko Da Ƙarshen Kalma

Ƙari a farko da ƙarshen kalma, ƙari ne da ake yi wa kalma a farko da ƙarshenta domin a samu wata sabuwar kalma mai ma’ana daban da wadda ake da ita. Wannan ƙari ana yinsa ne a farko da ƙarshen kalma. Ga misalin ƙarin da ake yi a farko da ƙarshen kalma:

Kalma

Ƙari

Sabuwar kalma

Su

Ma + su + nci

Masunci

Ƙi

Ma + ƙi + yi

maƙiyi

So

Ma + so + yi

Masoyi

Ha’inci

Ma + ha’inci + ya

Maha’inciya

Ƙarya

Ma + ƙarya + ci

Maƙaryaci

Ƙarya

Ma + ƙarya + ciya

Maƙaryaciya

Zamba

Ma + zamba + ci

Mazambaci

Yaudara

Ma + yaudari + ya

Mayaudariya

Mota

Mai + mot + oci

Mai-motoci

Rubutu

ma + rubu + ci

marubuci

 Aikin Gida:

Me ake nufi da sauye-sauyen kalmomi?

1.     Sauya waɗannan kalmomi a samar da wasu ta hanyar yin ƙari a farkon Kalma:

Gilashi

Aiki

Aski

Tafiya

Roƙo

2.     Sauya waɗannan kalmomi a samar da wasu ta hanyar yin ƙari a ƙarshen kalma:

Zaki

Allo

Maiki

Malam


Post a Comment

0 Comments