Talla

A1.3 Sauƙaƙon Jimloli

 

A jagoranci ɗalibai su san ma’anar jimla, su san rabe-raben jimla sannan su iya bambance tsakanin sauƙaƙƙar jimla da hardaɗɗiyar jimla, a ba ɗalibai misalai da dama ta yadda za su iya kawo sauƙaƙƙar jimla da kan su, ayi masu tambayoyi don tabbatar da ingancin abinda suka karanta. Ayi amfani da litattafai da taswirar jimla wajen koyar da ɗalibai.

Ma’anar Jimla

Jimla haruffa ne da ake haɗa wa watau baƙi da wasali don a samar da kalma, sannan a haɗa kalmomi domin samar da jimla mai ɗauke da gaɓoɓi. Watau dai in aka ce jimla ana nufi kalmomi ne ko gaɓar kalmomi da aka jerantawa domin samar da jimla mai ma’ana. A kan samu ɓangarori guda biyu su bayar da cikakkiyar ma’ana a cikin jimla, wasu lokuttan kuwa a kan samu gangarori fiye da biyu don gina jimla mai cikakkiyar ma’ana.

 Akwai ɓangaren suna da ɓangaren aikatau, wani lokacin kuwa akan samu ɓangaren suna da ɓangaren aikatau da ɓangaren wanda aikin ya faɗa mawa.

Rabe-Raben Jimla

Jimla ta rabu gida biyu, akwai sassauƙar jimla, akwai kuma harɗaɗɗar jimla.

Sauƙaƙƙar jimla ita ce jimlar dake zuwa da gaɓa biyu masu sauƙi. Wannan jimla ta kan yi bayani ne cikin sauƙi, kuma a taƙaice. Sauƙaƙƙar jimla ta kasu gida biyu, su ne kamar haka.

 

Jimlar Bayani: Ita ce jimlar da ke yin bayani kan abinda aka aikata. Misalai:

Ibrahim ya ci abinci.

Rabi’u ya je makaranta.

Lado ya sha ruwa.

 

Jimlar Tambaya: Jimla tambaya jimla ce da ke yin tambaya cikin sauƙi kuma kai tsaye. Ita wannan jimla ta kan zo da alamar tambaya ‘?’ daga ƙarshen jimlar.

Misali:

Ina Rabi’u ya je?

Me Ibrahim ya ci?

Me lado ya sha?

 Jimlar Umurni: Jimlar umurni jimla ce da ke yin umurni kan wani abu.         Misali:

Ɗauko ruwa.

Ci abinci.

Ɗauki kayan makaranta.

 Ɗaliabi su lura cewa, sauƙaƙƙar jimla ta kan zo da gaɓa biyu.

 Harɗaɗɗiyar jimla ita ce jimlar da ke zuwa da gaɓa uku ko ma fiye da haka waɗanda suka harɗe da junansu. Misali akwai jimla wadda ke ɗauke da suna da aiki da kuma wanda aiki ya faɗa mawa.

 

Misalan Jimloli

Misalin sauƙaƙan jimloli masu ɓangaren suna da aikatau:

Ɓangaren Suna

Ɓangaren Aiki

Cikakkiyar Jimla

Ɗalibai

Suna karatu

Ɗalibai suna karatu.

Ɗalibar

Ta tafi gida

Ɗalibar ta tafi gida.

Malami

Yana rubutu

Malami yana rubutu.

Yaro

Ya sha ruwa

Yaro ya sha ruwa.

Ibrahim

Ya ɗauki wayarsa

Ibrahim ya ɗauki wayarsa.

Mustapha

Yana wasa da komfuta

Mustapha yana wasa da komfuta.

 

Misalin sauƙaƙan jimloli masu ɓangaren suna da aikatau da wanda aiki ya faɗa mawa:

 

Ɓangare Suna

Ɓangaren Aiki

Wanda aiki ya Faɗa Mawa

Cikakkiyar Jimla

Ibrahim

Ya kashe

ɓera

Ibrahim ya kasha ɓera.

Salisu

Ya ci abinci

A cikin kwano

Salisu ya ci abinci a cikin kwano.

Harisu

Ya buga kwallo

A cikin gwal

Harisu ya buga kwallo a cikin gwal.

Malami

Yana rubutu

A bisa allo

Malami yana rubutu a bisa allo.

Bello

Ya zauna

Bisa kujera

Bello ya zauna bisa kujera.

Mohd

Ya ɗora abun wasa

Bisa teburi

Mohd ya ɗora abun wasa bisa teburi.

Abdallah

Yana wasa

Da keke

Abdallah yana wasa da keke.

 

Ɗalibai su kula cewa, a waɗancan misalai na sama harɗaɗɗun jimloli masu ɓangaren suna, aikatau da wanda aiki ya faɗa mawa, in an cire ɓangaren wanda aiki ya faɗa mawa, za a samu cikakkiyar jimla mai ma’ana ko marar ma’ana.

 

Aikin Aji:

1.     Rubuta sauƙaƙƙar jimloli guda biyar.

2.     Rubuta jimlar bayani guda uku.

3.     Rubuta jimlar tambaya guda uku:

4.     Rubuta jimlar umurni guda uku:

 

Post a Comment

0 Comments