Talla

A1.2 Kalmomi Masu Ma’ana Ɗaya

 

Ɗalibai su bayyana kalmomi biyu ko fiye da haka masu ma’ana ɗaya. A yi amfani da litattafai da hotuna da katuttuka da jadawali. A yi tambayoyi daga ƙarshen darasi.

Bayyana kalmomi Masu Ma’ana Ɗaya

Misalan kalmomi biyu masu ma’ana ɗaya:

Kalmomi

Kalmomi Masu Ma’ana ɗaya

Hanya

Titi

Riga

Taguwa

Rafi

Gulbi

Kogi

Ƙorama

Dakata

Jira

Saurara

Ji

Mutuwa

Rasuwa

Mage

Kyanwa/kuliya

Babba

Ƙato

Hula

Tagiya

Kofi

Moɗa

Ƙofa

Ƙaure

Azure

Garka

Kewaye

Banɗaki

Aji

Ɗakin-karatu

Baba

Abba

Mama

Umma

Iccen bedi

Iccen dalbeji

Wayar-tafi-da-gidanka

salula

Riga

Taguwa

Babur

Mashin

Koko

Ƙullu/kamu

Karin safe

Kumallo/kalaci

Liƙe/liƙo

Kari

Rufi

Shigifa

Ƙorama

Tafki

Aikin Aji

  1. Bayyana kalmomi masu ma’ana ɗaya guda biyar

 

Post a Comment

0 Comments