Talla

A1.2 Auna Fahimta

 Auna Fahimta

Ɗalibai sui ya karanta labarai sannan su ba da labarai na kansu, sui ya sake tsara labaran da suka karanta da kansu ko suka saurara, sannan su san ma’anonin wasu zaɓaɓɓun kalmomi da aka yi amfani da su a cikin labaran. A jagoranci ɗalibai wajen kawo masu labarai da jawabai da batutuwa sannan a fitar da kalmomi masu tsauri da bayanansu, a yi tambayoyi sannan a gyara masu aikin da aka basu. Ayi amfani da litattafai ko jaridu ko talabijin ko rediyo wajen koyarwa. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

Auna fahimta na nufin gwaji ko jaraba kaifin tunani da fahimtar ɗalibai a kan abinda suka saurara ko suka karanta daga litattafai ko ƙasidu ko rikoda. Ta hanyar gwada kaifin tunani da fahimtar ɗalibai ne ake gane ƙoƙarinsu da kuma kaifin tunaninsu wajen iya tuna abinda suka saurara ko suka karanta. Akwai matakan da ɗalibai ya kamata su bi kafin nuna kwazonsu, matakan sune kamar haka:

Sauraro cikin natsuwa, ɗalibai su kasa kunne su saurari labaran da ake karanta masu cikin natsuwa, ya maida hankalinsa waje ɗaya sannan ya saurara sosai a yayin da ake karanta jawabai ko labarai, wannan zai tamaka masa ya iya riƙe duk abinda ya saurara.

Fahimtar tambaya na taimakawa sosai wajen bayar da kyakyawar amsar don haka a fahimci tambaya sosai kafin bayar da amsarta.

Ɗalibai su riƙa amfani da ingantacciyar Hausa waje karatu ko wajen magana a cikin Hausa, wannan na taimakawa ɗalibai su fahimta sannan su iya bayar da amsa ta yadda za a fahimce su.

 A karanta waɗannan bayanai da ke biye don ɗalibai su saurara sannan a basu dama su sake karantawa a cikin zuci ko a bayyane su kuma bayar da amsoshin tambayoyin da ke ƙasa:

Can wani zamani da ya gabata, lokacin turawa sun fara shigowa ƙasashen Afrika, suna kwashe dukiyar yankin suna raya ƙasashensu da ita. Har ma Turawan Ingila sun fara kwararowa ƙasar Najeriya, ƙasa mai tarihi da al'umma da ƙabilu da ma'adanai na cikin ƙasa da kuma na saman ƙasa. Sun riƙa mulkar ƙabilu sannan su ka kafa makarantu. Ko a wannan lokaci kuwa, ƙasar Hausa ta shahara wajen salon mulki. A ƙasar Hausa kuwa sun kafa makarantar farko a Daular Kano Mai suna ‘Makarantar Ɗan Hausa’, sannan suka damka wa wani baturen Ingila mai suna James Rechard riƙon makarantar.

A wannan zamani, anyi wani shahararren Malamin Duba a ƙasar Katsina, shahararsa kuwa da zagaye duk ƙasar Hausa da ma sauran kasashen sauran ƙabilu. Wannan Malamin Duba kuwa ya iya sarrafa baƙi ya koma fari sannan ya maida azurfa ta zama zinari.  Ko hukumci za a yanke a cikin fada sai an tuntuɓi wannan malamin. Wannan malami kuwa babu abinda yake so face ‘ya’ya amma Allah bai bashi ba, har sai da rayuwarsa ta yi nisa, ya faɗa gangarar tsufa, jikinsa ya yi laushi, sai da sanda ya ke doddogara ya yi tafiya sannan Allah ya ba matarsa ciki.

Lokacin da Turawa su ka ci ƙasar Hausa da yaƙi, suka kafa makarantun boko, sannan suka riƙa kama yara suna tursasa su shiga makaranta, sai Malam mai gani har bayan rai ya juya wa Sarki baya a kan harkokin Turawa sannan ya yi ƙaura ya tashi daga cikin garin Katsina ya koma wani ruƙuƙin daji ya gina gida sannan ya yanki gona, wannan ruƙuƙin daji kuwa shi ne ya koma garin ‘Yandaka wanda ya jingina da dajin Rugu.

Bayan wata tara kuwa, matar Malam Mai Gani har bayan rai ta haifi ‘yan tagwaye dukkansu maza, da ranar bakwai ta zagayo Malam ya tara mutanen ɓoye watau bara’izai aka sha shagali sannan aka raɗa wa yara suna Karambani da Karambana.

Bayan yara sun yi wayo sun zama samari, wata rana suka saci jiki suka shiga gari yawon buɗe ido, a ranar kuwa anyi sa’a gimbiya ta fito yawon shaƙatawa bisa dokinta mai suna danda wanda take tsananin so. Ta sha ado da tagulla da zinari da azurfa, dokinta kuwa sai sheƙi yake yi, anyi masa ado da wani irin farin ƙarfe da siliki sai walkiya suke yi. Gimbiya kuwa ba a maganarta wajen kyawo, tana da kyan sura tun daga sama har ƙasa. Tana ta shawagi cikin gari, ga bayi nan zagaye da ita, tana cikin kilisa sai ta haɗu a su Karambana. Suna ganinta kuwa sai suka kudurce a ransu sai sun shiga gidan sarki. Tun lokacin da Karambana ya gyalla ido akan gimbiya begenta ya soki zuciyarsa, shi kuwa Karambani ba komai yasa yake son shiga gidan sarki ba sai don ya sace dokin gimbiya watau danda.

Ɗalibai su haddace sannan su naƙalci waɗannan muhimman kalmomi da jimloli:

 

Kalmomi ko Jimloli

 

Ma’anarsu

Karambani ko Karambana

Yaro wanda ya cika wauta ta ɓangaren matsi don sanin wani abu wanda bai sani ba.

Danda

Doki ne mai launin fari da baƙi a jikinsa.

Gimbiya

Ɗiyar sarki.

Barga

Inda ake turke dawakai.

Jakar kuduri

Jaka ce da ke sihirta duk abinda ake so a cikin labarin.

Kofar ‘yanɗaka

Ƙofa ce a birnin Katsina wacce ake bi a fita daga garin sannan a nufi garin Batsari ko ‘yanɗaka.

 Tambayoyi

  1. Yi taƙaitaccen bayani da bai wuce layi biyar ba ka bayyana irin adon da gimbiya ta yi:
  2. Sake rubuta labarin yadda karambani da Karambana suka shiga gidan sarki a cikin layi huɗu:
  3. Wani gari ne aka fara ƙafa makarantar boko?
  4. Ya sunan makarantar?

An ciro wannan labari daga littafin ‘Karambana ko kaga Dokin Sarki’ wanda Bello Hamisu Ida ya rubuta a shekarar 2018 wajen kos din bitar kagaggun labarai wanda Pleasant Library haɗin guiwa da Makarantar Malam Bambadiya suka shirya wa wasu haziƙan marubuta.

Ranar Samun ‘Yancin Kai A Nijeria

Ranar samun ‘yancin Nijeriya rana ce ta hutun aiki da ake gudanarwa a ƙasar Nijeriya wanda ake murna da shagulgular samun ‘yancin kai a ranar ɗaya ga wata oktoba ta kowace shekara. A shekarar 1914 ne turawan mulkin mallaka suka haɗe kudancin ƙasar da arewacin ƙasar inda suka shimfiɗa mulkinsu, waɗannan wajaje sune yanzu suka zama ƙasar Nijeriya. A cikin shekarun 1950 ne masu rajin samun ‘yancin kai suka fara fafutukar neman ‘yanci daga wajen turawa. Bayan shekaru uku da fara neman ‘yancin kai, sai aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima sannan aka ba ƙasar tuta mai nuna alamar cin gashin kan ta. Lokacin da ‘yan ƙasar suka sauya tutar birtaniya suka kafa sabuwar tutar Nijeriya domin nuna murnar samun yanci daga turawa a ranar ne ɗaya ga watan oktoba shekara ta 1960.


Tarihi ya nuna cewa, an shafe shekara da shekaru ‘yan kishin Najeriya na ta gwagwarmayar kwato wa ƙasar tuta daga hannun Turawan mulkin mallaka na Burtaniya. Sir Abubakar Tafawa Balewa wanda ya zamo Firaministan Najeriya na farko ne ya karɓi tutar ‘yancin ƙasar daga hannun gwamna janar Sir James Willson Robertson, wanda ya mulki Najeriya daga shekarar 1955-1960.

 Bayan da ƙasar ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960, sai aka kafa gwamnati, inda bisa tsari Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ya kamata ya zama Firaminista, amma sai ya marawa mataimakinsa baya wato Sir Abubukar Tafawa Balewa wanda ya zamo Firaministan farko, shi kuma Dr. Nmandi Azikwe gwamna na farko a Najeriya.

Kafin ranar, a ranar juma'a, za a gabatar da lacca, da addu'o'i bayan sallar juma'a a babban masallacin ƙasa. Sai kuma a ranar asabar, sai mabiya addinin kirista su yi addu'o'in nuna godiya ga ubangiji, a yammacin ranar  lahadi ta gab da ranar ɗaya ga watan oktoba, da misalin ƙarfe huɗu a babbar cibiyar bauta ta ƙasa. Sojoji na gudanar da ɗan kwarya-kwaryan bikin nuna bajinta a fadar shugaban ƙasa.

‘Yan ƙasar na yin tattaki zuwa filin Tafawa Balewa dake Jihar Legas domin ganin yadda shugabannin farko na ƙasar suka amshi takardar ‘yanci daga Sarauniyar Ingila wanda a lokacin gimbiya Kent Aleɗandria ta wakilta. A ranar kowa murna ya ke yi, a kan yi shagulgula tare da ifice-ifice na nuna farin ciki, yanzu kuwa da zamani ya zo, a kan ɗauki hotuna da rigunan ƙasar ko tufafi masu launin fari, tsanwa da fari don nuna farin ciki da murna. Wasu kuwa kan watsa hotunansu tare da fatan alƙairi ga ƙasar a kafafen sadarwa na zamani.

A ranar shugaban ƙasa kan yi jawabi ga ‘yan ƙasa tare da nuna godiyarsa da kuma jadadda ƙudurorinsa na ci gaba, sannan kuma sojoji kan yi fareti da wasanni don nuna farin ciki, a kan raira taken ƙasar har na tsawon lokaci don tunawa da mazan jiya.

‘Yan Nijeriya suna murnar cika shekara hamsin da tara 59 da samun ‘yancin kai daga mulkin mallakar turawa a ranar ɗaya ga watan oktoba. Ana fara shagulgula ne bayan shugaban ƙasa ya gama jawabi a fadarsa wanda ake watsawa a kafafen yaɗa labarai kamar: gidajen radiyo, gidajen talabiji, jaridu, kafar sada zumunta da sauransu.

 Muhimman Kalmomi

Ɗalibai su haddace sannan su naƙalci waɗannan muhimman kalmomi da jimloli:

 

Kalmomi da Jimloli

 

Ma’anarsu

Ranar samun ‘yancin kai

Rana ce da ‘yan ƙasar Nijeriya suka samu ‘yancin cin gashin kansu, ana murnar zagayowar ranar duk shekara.

Burtaniya

Ƙasa ce da ta mulki ƙasar Nijeriya, ƙasa ce ta fararen fata wacce sarauniya ke mulki.

Masallaci

Inda musulmai ke gudanar da bautarsu.

Babbar cibiyar bauta

Coci inda kirista ke gudanar da bautarsu.

Kafar sada zumunta

Kafafen sada zumunta na soshiyal midiya waɗanda su ke a intanet.

Tuta

tuta ce da ‘yan ƙasar Nijeriya mai launin fari, tsanwa da fari.

Takardar ‘yanci

Takarda ce da aka amince da ba ‘yan ƙasa damar cin gashin kansu.

Shagulgula

Shagulgula jam’i ne na shagali wanda ke nufin yin biki tare da nuna murna da farin ciki.

Mazan jiya

Sojoji da farar hula waɗanda suka yi gwagwarmaya don kwato ‘yancin.

 

Tambayoyi

1.     ƙasar Nijeriya?

2.     ɓi tutar Nijeriya a hannun Burtaniya?

3.     ƙasar Nijeriya?

     ƙaitaccen bayannin da bai wuce layi biyar ba a kan yadda aka gudanar da bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai a garinku? 

 

Post a Comment

0 Comments