Talla

A1.1 Tsarin Sassauƙar Jimla


Ɗalibai su tantance sassan sassauƙar jimla, su san ma’anar jimla a taƙaice su iya bayanin sasssauƙar jimla da kawo misalan sassauƙar jimla. A yi amfani da litattafai da rediyo da katuttuka wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

 Ma’anar Sassauƙar Jimla

Sassauƙar jimla ita ce jimlar da take ɗauke da sassan jimla biyu kacal; yankin suna da yankin aiki. Sassauƙar jimla, jimla ce da ta ƙunshi suna da abin da aka faɗi game da suna, watau aikin da sunan ya aikata, misali:

Audu ya sayi littafi

Indo tana share gida

Lado ya ɗauki takalmi

 Dukkan jimloli 3 da aka kawo misalin da yake sama sauƙaƙan jimloli ne. Sassauƙar jimla sun kasu gida biyu: jimla mai aikatau da kuma jimla maras aikatau. Abin nufi, sassauƙar jimla mai aikatau da kuma sassauƙar jimla maras aikatau.

 Sassauƙar Jimla Mai Aikatau: Ita ce jimlar da take ɗauke da kalmar aiki ko aikatau ko kuma aka aikata wani aiki a cikinta, wanda yake fita a yankin aiki na cikin jimlar.

            Misali:

Musa ya ɗebo ruwa

A cikin wannan jimla musa ne suna, ya aikata aiki watau ya ɗebo ruwa.

 Sassauƙar Jimla Marar Aikatau: Ita ce jimlar da babu aikatau a cikin yankin bayaninta.

            Misali:

Musa mutum ne mai surutu.

A cikin wannan jimla babu aikatau a cikinta.

 Bayanin Sassauƙar Jimla

Sassaukar jimla tana nufin jeren kalmomi waɗanda suke bayar da cikakkiyar ma’ana ga mai sauraro, sasasuƙar jimla kalmomi ne guda biyu ko uku ko hudu da ake jerantawa domin a samar da jimla mai cikakkiyar ma’ana.

Ga misalin yadda aka gina waɗancan sassauƙar jimlar:

Audu + ya + sayi littafi

Indo + tana + share gida

Lado + ya + ɗauki takalmi

 Waɗancan jimloli da suka biyo baya, in an lura jimlolin sun ƙunshi suna da kuma abin da aka faɗi game da suna.

 1. Audu ya sayi littafi

A jimla ta farko, audu ya sayi littafi, a wannan jimla Audu ne suna, haka kuma jimlar tana bayyana aikin da audu ya aikata, watau abin da aka faɗi game da suna, watau ya sayi littafi.

 2. Indo tana share gida

A jimla ta biyu, indo tana share gida, a wannan jimla Indo ce suna, haka kuma jimlar tana bayyana aikin da indo ta aikata, watau abin da aka faɗi game da suna, watau ta na share gida.

 3. Lado ya ɗauki takalmi

A jimla ta uku, lado ya ɗauki takalmi, a wannan jimla Lado ne suna, haka kuma jimlar tana bayyana aikin da lado ya aikata, watau abin da aka faɗi game da suna, watau ya ɗauki takalmi.

 Ga wasu misalan sassauƙar jimla:

  1. Musa mutum ne mai surutu.
  2. Rago ɗaya ne a turke.
  3. Indo ta sayi litattafai.
  4. Bello yana rubutu.
  5. Aisha ta tafi makaranta.
  6. Baba yana noma.
  7. Yara suna wasa.
  8. Musa yana wasa da mota.
  9. Wannan farar mota ce.

 Aikin Aji

  1. Rubuta sassauƙar jimla guda biyar.
  2. Tantance sassauƙar jimla cikin waɗanda aka rubuta.

 


Post a Comment

0 Comments