Talla

A1.2 Insha’in Baka: Marubuci Bello Hamisu Ida

 

Insha’in Baka

Xalibai su san ma’anar insha’in baka, ya kasance an jagoranci xalibai su saurari bayanai ko labarai waxanda ke da tambayoyi a ƙarshe sannan su bayar da amsoshi. A yi amfani da kaset ko faifan CD da talabijin ko bidiyo ko rikoda wajen sauraron labarai.

Ma’anar Insha’in Baka

Insha’i gajeren rubutu ne wanda ya kasance labari ko bayani ko wasiƙa ko muhawara. Daga cikin abinda aka rubuta yana iya zama na gaske watau tabbatace wanda ya taɓa faruwa ko kuma ƙagagge wanda aka ƙirƙira. Ana koyon dabarun rubutu ta hanyar insha’i.

 

Insha’in baka shi ne insha’i da ake bayar da labarin faruwar wani abu, a rubuta wani gejeren rubutu da ke baiwa mai karatu labarin wani abu daya faru a baya na gaskiya ko wanda aka ƙirƙira.

 

Xalibai su karanta waxannan labarai da ke biye, sannan su amsa tambayoyi da za su biyo bayan labaran:

 

Labarin Dattijo, Saurayi Da Budurwa

Can wani zamani da ya gaba ta, Kasuwar Katsina ita ce babbar kasuwa a duk faxin Ƙasar Hausa. Mutane daga ƙasashe daban-daban suna zuwa cin kasuwa.

 An yi wani Dattijo mai tarin dukiya ga tausayin mutane da taimakon talakawa, kullum za a iske shi zaune bisa kujera a zauren gidansa, tare da wani bawansa ya zauna ƙasa suna fira. Har ƙasashen Larabawa yake zuwa yin fatauci irinsu Saudiya da Sudan, duk kuwa lokacin da ya yi aniyar fita fatauci ayari da dama kan bisa su damƙa masa amanar dukiyarsu saboda riƙon amanarsa. Babbar xabi’arsa ita ce, son dabbobi, duk inda za shi dabbobi ne abokan rakiyarsa, duk kuwa abin da  ya ci sai ya ba dabbobinsa irinsa. Akwai wata barewa da yake tsananin so a cikin dabbobinsa.

 


Wata rana Dattijo ya shirya ya yi aniyar tafiya Sudan yin fatauci, ya shirya raƙumansa da alfadarai, ya xora masu kaya niƙi-niƙi, ya gama shiri ya hau wata amintacciyar goxiyarsa. Bayan La’asar ya fita ta ƙofar Sauri don neman sa’a. Bakin ƙofa ya haxu da wani Saurayi haye bisa dokinsa danda riƙe da keji guda biyu, xaya ɓera ke cikinsa xaya kuwa mage ce cikinsa.

 

Su ka yi gaisuwa sannan suka yi gaba, suka sake haxuwa da wata Budurwa, tana sanye da wani farin mayafi, ta yi masu sallama sannan ta tambayi shugaban ayari, Dattijon ya karɓe ta cikin aminci, suka yi gaba tare.

 

Suna cikin tafiya sun keta sahara ta farko, sun shiga wata sarƙaƙiyar daji, suka samu waje suka yada zango ƙarƙashin wata itaciya. Madugu ya fiddo gurasa da zumuwa suka ci su ka yi ibadarsu sannan suka sake nausawa cikin daji suna ta addu’o’i. Suna cikin tafiya ‘yan fashi suka tare su, suna riƙe da muggan makamai sai mazurai suke yi, aka ja Datijjo, da saurayi da budurwa zuwa gaban sarkin ɓarayin, aka xaure su sannan aka duƙar da su gaban sarkin ɓarayi.

 

Ya harare su ya ce masu; “Ku ne ku ka sace mani dukiya?”

Dattijo ya ce, “Ba mu yashe maka dukiya ba.”

Sarkin Ɓarayi ya ce, “Ta cikin saharar da ku ka biyo na aje dukiyata, in kuwa ba ku fiddo ta ba sai na fille maku kawuna, ke kuwa ki zama matar Sarkin Ɓarayi”

Sarkin ɓarayi ya kalli Dattijo  ya ce, “Za ka iya ceton ranka da hikaya?”

 

Dattijo ya yi nutso cikin tunani sannan ya fara ba da labari da cewa.[1]

Tambayoyi:

1.    A wancan zamanin, wace kasuwa ce babbar kasuwa a ƙasar Hausa?

2.    Wane dalili yasa kasuwar garin Katsina ta zama babbar kasuwa?

3.    Lisaffa ƙabilun da ke zuwa cin kasuwa a ƙasar Katsina?

4.    Yi taƙaitaccen jawabi kan halayyar wannan dattijo?

5.    Cike waxannan guraben:

 

6.    Bayan la’asar ya fita ta _____________ don neman sa’a.

7.    Saurayi haye bisa _______ riƙe da _________________.

8.    ___________ ya fiddo __________ da zumuwa suka ci.

9.    Suna cikin tafiya sun keta ________ ta farko.

10.                       Ya harare su ya ce masu; “________________________?”


11.                        

Hikayar Dattijo

Allah ya yi mani sha’awar kiwata dabbobi, cikin gidana ba ka rasa dabbobi danginsu, tsuntsaye; tantabara, kurciya, dawisu, aku, agwagwa, ɓangaren tumaki; tunkiya, akuya, raguna, xan-taure, shanu da raƙuma, ina kiwata; dawakai, mage, da namun daji, cikin namun dajina, akwai wata barewa mai hankali da nake tsananin so.

 


Wata rana barewata ta fita kiwo da safe maciji ya sare ta, ta faxi tana nishi, ni kuwa da na ga marece ya yi barewa ba ta  dawo ba, sai na shiga daji nemanta. Haka na iske ta tana ta nishi rai hannun Allah, na sungume ta ina hawaye na nufi gida, amma kafin in kai gida rai ya yi halinsa, na sauke barewa ina ta kuka. Da yake gab da Magriba, har duhu ya fara shigowa. Ina cikin kuka na ji wani irin rugugi ƙasa ta rinƙa girgiza, wata shirgegiyar Aljana ta tsaga ƙasa ta fito.

 

Ban tsorata da ita ba, na ci gaba da kuka raina na raxaxin rasa barewata, aljana ta yi gyaran murya sannan ta ce mani; “Bawan Allah kana da tausayi da kula dabbobi, abin da  ba ka sani ba shi ne, wannan barewa ba mutum ba ce Aljana ce ta yi laifi Sarauniyar Aljanu ta mayar da ita barewa, ka kasance mai adalci don haka za mu saka maka da alheri, za mu ba ka wata barewa mai riƙon amana” Aljana ta ci gaba da cewa, “Goxiya za ta sauko daga sama ta xauke ka ta kai ka wata duniya”

 

Aljana na kawowa nan sai ta ɓace. Na dai ci gaba da kuka, kafin wani lokacin sai barewa ita ma ta ɓace, nan fa hankalina ya tashi na shiga neman barewata, ina cikin nema sai ga wata goxiya ta sauko daga sama da fukafukai, ta yi haniniya ta miƙe ta dire ƙafafuwanta gabana, tana duƙawa gabana ta saɓe ni sai gani bayanta, ta sake yin haniniya ta ruga da gudu ta tashi sama muka lula cikin sararin samaniya.

Muka ci gaba da tafiya har muka ratsa ruwan Bahar Maliya, sannan muka sauka saman wani tsibiri. Muna sauka wasu zakuna suka taso mana, na ruga da gudu. Ina cikin gudu wata sarauniya ta tari gabana, tana sukuwa bisa wani ingarman kure.

 

Na tsaya ina mamaki, Sarauniya ta tare ni cikin murna ta ce, “Muna maraba da zuwanka”

 

Ta kai ni fadarta, duk illahirin fadar dabbobi ke yi mata hidima. Maguna su ne masu tsaron gida, su kuwa zakuna tsibirin baki xaya suke tsaro. A cikin gidan akwai tsuntsaye masu rera waƙoƙi da muryoyi irin na su xawisu da aku wanda ya ratsa ƙasar Hausa don iya surutu. Su kuwa ɓeraye su ne masu girka abinci, aka kawo mana abinci muka ci. Abincin sai ka ce a Madina.

 

Sarauniyar ta kirawo ni, ta tambaye ni, na kwashe labarina duka na gaya mata, da ta fahimci irin tsananin damuwa na rashin barewata da na yi, sai ta yi mani alƙawari za ta sana’anta mani wata Barewa wace ta fi wace na rasa. Ta jani xakin tsafinta, ta rinƙa tambaya ta siffar Barewata ina gaya mata, ita kuwa ta hura wuta, ta kawo wani garin magani, ta xauko ƙoƙon kai ta zuba ruwa sannan ta rinƙa fadar kalamai, daga ƙarshe ta tambaye ni kalar idanuwan Barewata, ni kuwa sai na kada baki na ce, “Idanuwanta kamar na zinariya”

 

Ta sana’anta mata idanuwan zinariya, sannan ta yi wasu sabbatu, tana gamawa sai ga wata kyakyawar barewa mai idanuwan zinare, duk lokacin da ta kalle ka sai ka ji tsigar jikinka ta tashi. Sarauniya ta sallame ni na hau godiya tare da barewa muka sake lulawa cikin sararin samaniya muka bar wannan tsibiri.[2]


 

Tambayoyi:

1.    Waxanne dabbobi ne datijjo ke kiwo?

2.    Wace dabba yafi sha’awa cikin dabbobinsa?

3.    Me ya samu dabbarsa a cikin jeji?

4.    Me aljanar ta yi wa Dattijo?

5.    Siffanta irin dabbar da ta sauko ta xauki Dattijo?

6.    Cike waxannan guraben:

 

7.    A cikin gidan akwai _______ masu rera ______________.

8.    Da muryoyi irin na su _____________ da ____________.

9.    Wanda ya ______ har ƙasar _______ don iya surutu.

10.                       Muka sauka wani ________, duk _________ ne a cikin tsibirin.

11.                       Ta kai ni _______, duk illahirin fadar _____ ke yi mata hidima.

 



[1] An ciro wannan labari mai suna ‘Labarin Dattijo, Saurayi da Budurwa’ daga littafin ‘Hikimarka Jarinka’ Littafi na Biyu wanda Bello Hamisu Ida ya rubuta

 

 [2] An ciro wannan labari mai suna ‘Labarin Dattijo, Saurayi da Budurwa’ daga littafin ‘Hikimarka Jarinka’ Littafi na Biyu wanda Bello Hamisu Ida ya rubuta

 

 

Post a Comment

0 Comments