ABUJA, NAJERIYA - Adadin man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu
da kashi 28%, tun bayan da shugaban kasar Bola Tinubu ya janye tallafin man a
karshen watan Mayu.
Cikin watan da ya gabata, man fetir din da aka sayar a
Najeriya na matsayin lita miliyan 48 ne da dubu 430, maimakon lita miliyan
66 da dubu 900 da aka saba kafin janye tallafin.
Man na fetir dai ya yi tsada a kasar sabanin yanda yake a
gomman shekarun da suka gabata, a kasa mafi karfin arziki a nahiyar Afirka.
Rahotanni ma daga kasashen Kamaru da Benin da Togo, na nuna cewa
'yan kasuwanni bumburutunman fetir sun durkushe tun bayan da aka janye tallafin
saboda tsadar makamashin a yanzu.
Dala biliyan 10 ne Najeriyar ta kashe a bara wajen biyan kudin
tallafin man.
Bankin duniya kuwa a gefe guda ya ce Najeriyar na iya adana
akalla biliyan biyar da miliyan 100 na dala daga janye tallafin da ma
sauye-sauyen da Tinubu ya kawo a fannin hada-hadar kudaden ketare.
0 Comments