ABUJA,
NIGERIA — Gwamnatin Tinubu ta Najeriya ta
bayyana wasu daga cikin kyakyawar manufofinta na cika alkawarin da ta dauka na
biyan basussukan da ake bin kasar, a yanzu gwamnatin ta shirya biyan bashin
dala miliyan 500 a watan Yulin 2023. Wannan ya nuna yadda
gwamnatin ta mayar da hankali kan alhakin kudi da kuma jajircewarta na ci gaba
da tabbatar da amincin Najeriya a kasuwannin hada-hadar kudi ta duniya.
Ta hanyar cimma wannan gagarumin biyan basussuka, Najeriya na da
burin bunkasa kwarin gwiwar masu zuba jari da kuma karfafa sunanta a matsayin
amintacciyar kasa mai karba da biyan bashi a fagen kasa da kasa.
Rahotanni daga ofishin kula da basussuka (DMO) na nuni da cewa,
Najeriya na shirin biyan dala miliyan 500 na Eurobond a wannan watan Yulin
2023, wanda ya yi daidai da sharuddan lamunin.
Kudirin wanda aka samu shekaru biyar da suka gabata akan kudi
kashi 6.375% a duk shekara, yanzu za a biya shi, domin ko dai Najeriya ta biya
bashin ko kuma ta kara kudaden da ake bukata.
Yawanci, ana biyan basussukan Eurobond daga asusun ajiyar waje
na kasar ko kuma ta hanyar asusu na musamman da aka kebe don biyan kudin waje.
Sai dai Najeriya ta fuskanci kalubale a wannan fanni, inda asusun ajiyarta na
waje ya ragu da kusan dala biliyan uku a bana, sakamakon raguwar sayar da
danyen mai. Bugu da kari, jawo hannun jari na kasashen waje ya sami tasgaro da
wahala, hakan yayi tasiri da rashin kudin.
To sai dai kuma, ba a taba samun shakku kan yadda kasar za ta
iya biyan bashin ba, duk da raguwar kudaden da aka samu, sabanin sauran
kasashen dake kudu da hamadar Sahara irin su Ghana, wadanda sai da suka sake
yin shawarwarin lamuni bayan sun gaza.
Rahotannin baya-bayan nan na nuni da cewa, basusukan da ake bin
Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 82 biyo bayan hadewar Naira tiriliyan 73
kafin hadewar.
Masana dai na ganin da wuya Najeriya ta nemi karin kudin Euro
saboda kalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta na rancen kudaden
kasashen waje. Sai dai kuma nasarar da aka samu na biyan bashin dalar Amurka
miliyan 500 na Eurobond ya sake tabbatar da aniyar Najeriya wajen tafiyar da
harkokin kudi da kuma sanya kasar nan a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya.
0 Comments