Hukumar yaki da cin hanci a Kano ta gayyaci tsohon gwamna jihar Abdullahi Umar Ganduje a kan badakalar dala domin amsa wasu tambayoyi don wanke kansa.
Hukumar
ta KPCACC a jihar Kano ta bayyana cewar za ta bi duk matakan da doka
ta tanada a kan tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje matukar ya
bijirewa takardar sammacin da ta aika masa.
Hukumar na son tsohon gwamnan Kanon ya bayyana a gabanta dan
kare kansa daga zargin karbar rashawa da ake yi mishi bayan ganin wani faifan
bidiyo a shekarun baya.
Shugaban hukumar Barr Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana
cewar suna sa ran tsohon gwamnan zai amsa gayyatar a makon gobe.
A shekarar 2017 ne aka fara sakin fefen bidiyon da ake zargin
Ganduje ne yake karbar sunkin daloli yana cusawa a cikin aljihunsa, zargin da
tsohon gwamnan ke musantawa ya na mai cewar fasahar zamani a kayi amfani da ita
wajen kirkirar bidiyon.
0 Comments