Daga: AREWA NEWS
SOKOTO, NAJERIYA - Wasu ƴan mata su goma sha sun rasa ransu bayan kifewar kwale-kwale a wani ƙauye mai suna Dandeji da ke ƙaramar hukumar Shagari dake jihar Sokoto.
An ruwaito cewa ƴan matan na kan hanyarsu ta zuwa wani daji da ke kusa domin neman itace lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a safiyar ranar Talata.
Shahararriyar Jaridar Daily Trust ce ta ruwaito cewa; ƴan mata sama da arba'in ne ke cikin kwale-kwalen lokacin da haɗarin ya faru.
Wani wanda abun ya faru a gabansa dake zaune a yankin mai suna Muhammad Ibrahim, ya ce, ya zuwa an gano gawawwaki 1, ya kuma ƙara da cewa, masu ninƙaya na ci gaba da neman sauran waɗanda suka rasu a haɗarin.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Shagari, mai suna Aliyu Abubakar, ya tabbatar da faruwar haɗarin, ya kuma ƙara da cewa ana shirin yi wa matan da suka rasu jana'iza.
0 Comments