Talla

Rundunar Sojojin Najeriya ta Ceto ‘Yan Matan Chibok Biyu

Daga: Arewa News

BORNO, NAJERIYA - Rundunar da aka fi sani da sunan Operation Haɗin kai sun ceto wasu daga 'yan mata biyu da aka sace a ƙaramar hukumar Chibok ta jihar Borno tun a watan Afrilun 2014.

Kodayake, dakarun sojojin sun sha ceto ƴan matan a hannun boko haram, saidai wannan ceton da suka yi na baya-bayan nan, an yi shi ne bayan shekaru tara da sace ƴan matan. ƙungiyar Boko Haram su ne suka kai hari tare da sace ‘yan mata 276 lokacin da suke rubuta jarabawar kammala sakandare a makarantar garin Chibok lamarin da ya ja hankalin duniya baki ɗaya.

Sojojin Operation haɗin kai sun samu nasarar ceto ‘yan matan a wani yanki na Boko Haram dake dajin Sambisa, ƴan matan sun ce, sunansu Esther Marcus da Hauwa Malta, dukkanninsu shekarunsu 26 da haihuwa.

A cewar rundunar, an ceto Esther tare da jaririyarta mai shekara ɗaya. Kuma ta yi aure har sau uku, kuma dukkan mazajen da ta aura ‘yan kungiyar da suka yi garkuwa da ita ne.

Ita kuma Hauwa Malta an ceto da cikin wata takwas, kuma ta haifi yaro a inda aka ajiye su ake kula da su kwanaki 10 bayan ceto su.

Sojojin sun kuma kashe sama da mutane 70 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a farmakin da suka kai a yankin Arewa maso Gabas.

Adadin 'yan matan da aka ceto yanzu ya kai 125, ciki har da 107 da 'yan ta'addan suka sako a shekarar 2018, uku da sojoji suka ceto a shekarar 2019, biyu a 2021, da 11 a 2022.

Post a Comment

0 Comments