Talla

Gwamnati za ta sa Ƙafa ɗaya da Masu Kwatar Waya a Kano

Daga: Arewa News

 KANO, NIGERIA — Gwamnatin jihar Kano ta ce tana sane da masu satar waya fa kwace kuma ta ɗauki matakan magance matsalar kwacen waya a hannu Jama’a da wasu batagarin matasa ke yi a wasu sassa na birnin. Haka kuma hukumomi a Najeriya sun fara bada shawara ga sabuwar gwamnatin ƙasar game da hanyoyin kawo karshen kalubalen tsaro a ƙasar.

Sai dai a ‘yan kwanakin nan wannan matsala tayi ƙamari, inda batagarin matasa kan yi fashin wayoyin hannun Jama’a masu tafiya a ƙasa ko kuma waɗanda ke kan ababen hawa.

 Wasu lokuta kuwa, ɓarayin kan haɗa kai da ƴan adaidaita, su yi satar waya da duk wanda ya shiga don a kai shi wani waje.

Wani ya shaida cewa, yana cikin tafiya bayan ya baro masallaci da asubahi, daidai kan wata kwana sai wata a daidaita ta tunkaro shi ɗauke da samari guda uku, suna ƙarasowa wajensa sai suka kai masa suka da wuƙa sannan sula tura shi cikin wani rami, in da ya samu rauni a hannunsa sakamakon wuƙar da suka soka masa, amma ba su samu damar kwace wayarsa ba, saboda ihun da ya yi. Sai suka ruka.

Sai dai hukumomin tsaro a jihar ta Kano sun ce wannan sabon kalubale nada alaƙa da shaye-shaye inda samarin kan sha su bugu kafin su fita aika ta ta'asar.

Manjo Mohammed Lawan El-Yakub na ɗaya daga cikin dubban mutanen da ke ba sabon shugaban ƙasa shawara a kan yadda zai ɓullowa lamarin rashin tsaro a ƙasar, ya kawo shawarar cewa, shugaban Najeriya mai jiran gado ya yi garanbawul a rundunar sojojin ƙasar data sama domin danka amanar yaƙi da kalubalen tsaro a hannun sahihan Jami’ai.

Post a Comment

0 Comments