Talla

An Kama Wasu Mata Kidnappers a Kano

Daga: Arewa News

KANO, NAJERIYA - An kama wasu mata a jihar Kano kan zargin satar yara da neman kuɗin fansa har miliyoyi bayan sin yi garkuwa da yaran.

A wata sanarwa wadda CP Abdullahi Kiyawa ya wallafa a shafinsa na fesbuk, ta ce, ƴan sanda sun ce sun kama wasu mata su biyu, da ake zargin sun shirya maƙarƙashiya tare da yin tuggun sace wasu ƙananan yara ciki har da ɗiyar ɗaya daga cikinsu, sannan suka nemi miliyoyin kuɗin fansa.

Cikin matan har da wata, mai shekara 45, da suke zargin tana cikin gungun mutum huɗu da suka sace wani yaro, tare da neman kuɗin fansa sama da naira miliyan biyar.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar, wato Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta zargi matar wadda gwaggon yaron ce, da shirya maƙarƙashiyar sace Almustapha Bashir a farkon watan jiya.

Ya ce tun da farko, mutanen da suka saci yaron, ɗan shekara shida ranar 4 ga watan Afrilu sun nemi mahaifinsa ya biya naira miliyan ashirin kafin su saki yaron.

Mahaifin da masu garkuwar sun daidaita a kan naira miliyan biyar da dubu ɗari da hamsin.

Ya ci gaba da cewa,

"Bayan gudanar da bincike, an kuɓutar da yaron ba tare da ko rauni ba, sannan an kama wadda ake zargi da shiryawa, da kuma tsara yadda za a sace Almustapha".

Haka kuma 'yan sanda sun kama duk waɗanda ake zargi da hannu a satar yaron, dukkansu matasa ne ƴan ƙasa da shekara talatin da haihuwa.

Post a Comment

0 Comments