Talla

Hukumar DSS ta kama mutume biyu kan zargin tayar da Tarzoma Kafin Zaɓen Gwamnoni a Kano

Daga: Mohd Abdallah

AREWA NEWS
KANO, NAJERIYA - Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta ce, ta kama wasu mutane biyu da take zargi da tunzura mutane domin tayar da hankali a jihar Kano gab da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha wanda za a yi a ranar Asabar.

An samu wata sanarwa da DSS suka wallafa a shafinta na Twitter in da hukumar ta ce, mutanen sun ɗauki wani bidiyo da suke yin bayanai na harzuƙawa da tunzura jama’a, sun riƙa wallafa bidiyon a shafukan sada zumunta.

Hukumar DSS ta wallafa sunayen Sharu Abubakar Taɓule mai shekara 37 a duniya, da kuma Isma’il Iliyasu Mnagu mai shekara 51 a matsayin waɗanda ta kama.

Ta kuma ce,

“Cikin waɗannan saƙonnin masu haɗari, sun nuna jam’iyyar siyasar da suke goyon baya kuma suka yi kira ga magoya bayansu su kai wa abokan hamayyarsu hari duk inda suka gansu.

Sun ƙara da cewa,
“Waɗanda ake zargin sun yi kira da a kai wa jami’an tsaro hari yayin zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi a ranar Asabar.
Saidai, Wata jam’iyyar siyasa a Kano na barazanar shirya zanga-zanga a sakamakon shirin kai hare-haren, in ji hukumar ta DSS.

Sanarwar ta ƙara da cewa jam’iyyar siyasar ta shirya kutsawa ofisoshin wasu hukumomin tsaro a ranar 16 ga watan Maris a matsayin nuna goyon baya ga waɗanda ake zargin.

Daidai lokacin da hukumar ke sanar da mutane kan wannan haramtaccen mataki da suka ɗauka, ta kuma yi kira ga jam’iyyar da ta dakatar da wannan aniya ko kuma ta shirya yaba wa aya zaƙinta.

DSS ba za ta zuba ido tana kallon mutane suna tunzura al’umma ba su tayar da hankali da rashin tsaro a jiha ba.

Sanarwar DSS ta ce za ta haɗa hannu da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da an samar da cikakken tsaron da zai bayar da damar gudanar da zaɓe mai inganci a jihar.

Baya ga Kano hukumar tsaron ta kama wasu mutane da ke irin wannan kiraye-kiraye a wasu jihohi a faɗin ƙasar.

Hukumar ta shawarci jam’iyyun siyasa a faɗin Najeriya da su gargaɗi mabiyansu su zama masu bin doka da oda, domin tabbatar da dimokuraɗiyya ta samu wurin zama yadda ya kamata.

Post a Comment

0 Comments