Daga: Mohd Abdallah
AREWA NEWS
GOMBE, NAJERIYA - An zargi wani malamin islamiyya da ɓata wasu ƴara su huɗu. Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ce ta sanar da kama Malamai, rundunar ta ce ta kama wani matashi mai shekara 38 kuna malamin Islamiyya bisa zargin lalata da wasu yara mata guda huɗu duka ƴaƴan mahaifinsu ɗaya.
Rundunar ta tabbatar da kama malamin kamar yadda mai magana da yawunta, DSP Mahid Mu’azu Abubakar ya yi ƙarin bayani.
A cewarsa yaran da abin ya rutsa da su ƴan shekara goma sha biyu ce da kuma ƴar shekara tara da kuma takwas.
Ya kuma ce, ba asalin malaminsu ba ne, yana zaune ne a makarantar Islamiyyar da yaran ke karatu, idan suka zo biya karatu, babban malami zai ce su je wajen wanda ake tuhuma da laifin domin su biya masa, sai ya yi amfani da wannan dama wajen yin lalata da yaran.
Ya kuma ce, an ɗauki lokaci matashin yana cin zarafin ɗaliban kasancewar yaran ƙanana ne da ba sa iya yi wa iyayensu bayanin abin da ke faruwa da su a makaranta.
Kakakin rundunar ya ce an kai ga gano lamarin ne bayan da aka samu; "ƙorafi da aka samu cewa akwai wata daga cikin ƴaƴan mutumin ƴar shekara 16 da wani mutum daban ya yi mata fyaɗe.
"Wanda ana fara wancan binciken ne har shi wannan ya fito wanda shi matashin mai shekara 38 ya kasance ya bayyana cewa yana lalata da yara ƙanana idan suka zo biya karatu a wajensa."
DSP Mahid Mu’azu Abubakar ya ce malamin ya bayyana masu cewa, wannan ne karon farko da aka same shi da aikata lamarin a kan yaran, saidai kuma saɓanin abinda ya yi iƙirari wannan ba shi ne na farko ba, ba na biyu ba kusan karo na uku kenan yana aikata irin wannan laifi.
A cewarsa, an kai yaran asibiti domin gudanar da bincike kan lafiyarsu yayin da shi wanda ake zargin aka tasa ƙeyarsa kotu domin fuskantar shari'a.
Kakakin ya kuma shawarci iyaye da su kasance masu jan hankalin ƴaƴansu tare da jansu a jika domin yaran su riƙa sakin jiki da su don su faɗa masu halin da suke ciki.
Ya kuma ce,
"Ko da ɗa namiji ne ka san ina ya je kuma me yake tafiya da shi, idan ba ka jan shi a jiki, ba za ka samu bayanin da ke faruwa a kan sa ba."
0 Comments