Talla

Yadda shirye-shiryen zaben shugaban kasa na 2023 suka kankama a jihohin Najeriya

Yayin da ya rage kwana guda kafin babban zaben shugaban ƙasa da na 'yan majalisun tarayya a Najeriya, shirye-shiryen tunkarar zaɓukan sun yi nisa inda jihohin ƙasar suka bayyana irin shirin da suka yi na zaɓe.

A Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin ƙasar, ana sa ran akalla masu kaɗa ƙuri’a miliyan biyu ne za su fita don kaɗa kuri’arsu a zaben shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisar tarayya da za a gudanar a ranar asabar.

Tuni hukumar zabe mai zaman kanta a jihar ta ce ta kammala rabon kayayyakin zabe na gama gari da kuma na musamman ga dukkan kananan hukumomi 21 da ke jihar.

A Abuja babban birnin tarayyar kasar ma, tuni ofishin hukumar zaben birnin ma ya aika kayan zaben zuwa kananan hukumomi shida da ke yankin, kuma an raba kayan ne da sa idon jami’an tsaro a ofishin hukumar zaben birnin.

Ita kuwa jihar Kaduna, wadda ke daya daga cikin jihohin Najeriyar da ke fama da matsalar tsaro, cewa ta yi baya ga kammala rabon kayayyakin zaben ga kananan hukumomin da suka dace, rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta shirya tsaf don samar da ingantaccen tsaro a lungu da sako na jihar.

A cewar rundunar ‘yan sanda dai tuni aka kammala horaswa tare da samar da isassun kayayyakin aiki ga jami’an tsaron.

Akalla jami’an ‘yan sanda dubu 16 ne za su yi aikin samar da tsaro a lokacin zabe a jihar ta Kaduna.

Ita ma makwabciyar Kadunan wato jihar Kano, hukumar zabe mai zaman kanta a jihar ta ce tuni ta kammala aikin raba mahimman kayan zabe zuwa matakin kananan hukumomin jihar 44.

Hukumar ta ce aikin da za a kama yanzu shi ne na tantacewa tare da wawware kayan zuwa matakin mazabu bisa sa idon wakilan jam’iyyu da jami’an tsaro.

A jihar Lagos ma, shirye-shiryen zaben sun yi nisa, inda aka ga karin matakan tsaro da hukumomi suka jibge don ganin an yi zaben lafiya cikin nasara.

Jihar Legas dai na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke da yawan mutanen da za su kada kuri’a, to sai dai ta kasance jihar da a kan fuskanci hatsaniya a lokutan zabe.

Post a Comment

0 Comments