KANO, NAJERIYA - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi zargin cewa sake fasalin Naira da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi manufa ce da aka shata da kudirin tauye dimokaradiyya. Ganduje ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da kungiyar tsaffin ‘yan majalisar dokokin kasar daga yankin arewa maso yamma, wadanda suka ziyarce shi don bayyana masa aniyar goyon bayansu ga dan takaran shugaban kasar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Zargin na
Ganduje ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya suke shan radadi sakamakon
karancin takardun kudaden Naira 200, 500 da 1000. A jawabinsa, shugaba Buhari ya ce sake fasalin Naira
ya samo asali ne daga kudirinsa na tada komadar tattaalin arzikin kasar,
rage hauhawar farashin kayayyaki da daakile halasta kudaden haram.
0 Comments