Daga: Bello Hamisu
ABUJA, NAJERIYA - A yau Laraba ne Kotun Kolin Najeriya za ta yanke hukuncin kan ƙarar da wasu gwamnoni suka shigar inda suke kalubalantar gwamnatin tarayya kan wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi.
A ranar 8 ga watan Febrairu ne kotun ta dakatar da gwamnatin tarayya na ayyana ranar 10 ga watan Febrairu a matsayin ranar daina amfani da amfani da tsofaffin kudin, abu kuma da Babban Bankin Ƙasar ya yi watsi da shi.
Gwamnonin jihohin Zamfara da Kogi da Kaduna ne suka fara shigar da ƙarar a kan Babban Attoni Janar na Ƙasa a ranar 3 ga watan Febrairu.
Daga baya ne kuma jihohin Legas da Ondo da Ekiti da Kano da Sokoto da Ogun da kuma Cross Rover suka biyo baya.
Sai dai lamarin ya ƙara tsananta ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, lokacin shugaban Muhammadu Buhari ya sanar da cewa tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1,000 sun daina aiki, inda ya ce a sake fito da tsohuwar takardar kuɗi ta N200 domin ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023.
0 Comments