KANO, NAJERIYA - Kotu a Kano ta sake tura Murja Ibrahim Kunya gida yari, bayan sake zaman ci gaba da shari'ar da ake mata. Haka zalika kotun ta kuma aike da Idris Mai Wushirya, Sadiq wanda ya yii wakar "A daidai ta nan" da kuma Aminu BBC zuwa gidan yari.
Rahotanni daga jihar Kanon na cewa, zauren malaman Kano ne ya gurfanar da matasan gaban kotu, bisa zarginsu da wallafa kalaman batsa a dandalin TikTok. Yanzu haka dai alkalin kotun ya tura su gidan yari har zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.
0 Comments