Bayan kaɗa ƙuri'a Wazirin Katsina Alhaji Ibrahim Ida kenan a majalisarsa tare da sauran al'ummarsa a majalisarsa dake ƙofar gidan mahaifansa a Bakin Kasuwa Galadunchi, Katsina.
Ya yin zaman, Wazirin Katsina ya yi adu'o'i ga ƙasa sannan ya ka hankalin matasa da su yi zaɓe cikin lumana ba tare sa jan hankali ba. Wazirin ya bayyana matasa masu tada tarzoma a ya yin zaɓe da waɗanda ba su san abinda duniya take ciki ba, kuma ya yi kira sa irin waɗannan matasa da su hankalta.
______________________
Shugaba Buhari tuni dai ya koma Daura domin kaɗa ƙuri'a, Buhari zai kaɗa ƙuri'arsa a rumfar zaɓe da ke kusa da gidansa a garin Daura tare da mai ɗakinsa Aisha Buhari.
______________________
A yau ranar 25 ga watan Fabrairu za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Sanatoci da ‘yan majalisar tarayya.
Sai kuma na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris.
Arewa News za ta kawo maku abubuwan dake faruwa a rumfunan zaɓe.
0 Comments