ABUJA, NAJERIYA - Hukumar zaɓen Najeriya ta gargaɗi jam'iyyun siyasa kan yaɗa sakamakon zaben shugaban ƙasar da na 'yan majalisun dokoki na tarayya.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin ƙaddamar da buɗe zauren tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Abuja babban birnin ƙasar.
Farfesa Mahmood ya ce hukumar INEC ce kawai doka ta ɗora wa alhakin fitar da sakamakon zaɓen.
“Ina kira ga jam'iyyun siyasa da kafofin yaɗa labarai da su ɗauki alkaluman sakamakon daga sakamakon da muka sanar, a matsayinmu na waɗanda doka ta ɗora wa alhakin fitar da alkaluman sakamakon zaɓen'', in ji Farfesa Mahmood.
A jiya Asabar ne dai hukumar ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokoki na tarayya.
Hukumar na gargaɗin ne a daidai lokacin da sakamakon zaɓukan ke ci gaba da fitowa.
0 Comments