Talla

Farashin man fetur ya ƙaru da kashi 55 a watan Janairu – NBS


ABUJA, NAJERIYA - Hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce farashin man fetur ya ƙaru da kashi 55 a watan Janairu.

Wannan na kunshe ne cikin wani rahoto da hukumar ta fitar, inda ta ce a watan na Janairu, 'yan Najeriya sun biya N257.12 a kan kowace lita.

Rahoton ya nuna cewa farashin a watan Janairun 2023 ya ƙaru da kashi 54.52 cikin 100 da kuma karuwar kashi 24.70 a kowane wata.

NBS ta kuma bayyana cewa jihar Imo ce ta fi kowace a sayar da litar man fetur, inda na ta ke a kan N332.14, sai Rivers a kan N327.14 da kuma Akwa-Ibom a kan N319.00. inda a arewacin Najeriya kamar Kano ake sayan mai a kan 350 duk lita, sai Katsina inda ake sayen lita kan 340.

Ta kuma lura da cewa Sokoto ce jihar da aka fi sayar da man fetur a kasan farashi, inda man fetur ɗin ke a kan N191.43 kan kowace lita, sai Filato a kan N192.14 da kuma Borno a kan N193.91.

'Yan Najeriya da dama na ci gaba da biyan sama da N185 kan kowace lita da aka amince da shi a matsayin farashin man fetur sakamakon ƙarancin mai, kamar yadda rahoton hukumar kididdiga ta kasa ya nuna.

 


Post a Comment

0 Comments