ABUJA, NAJERIYA - Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a dakin da ake tattarawa da sanar da sakamakon zaben kai tsaye ta kafafan yada labarai.
Jami’in sanar da zaben shugaban kasa kuma shugaban hukumar INEC, ya ce sakamakon jihohi 36 da Abuja ya nuna cewa, dan takarar shugaban kasa na jami’iyyar APC Bola Tinubu ya lashe zaben da kuri’u miliyan takwas da dubu dari bakwai da casa’in da hudu da dari bakwai da ashirin da shida (8,794,726).
Sai kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da ya zo na biyu, inda ya samu kuri’u miliyan shida da dubu dari tara da tamanin da hudu da dari biyar da ashirin (6,984,520).
Amma shi kuma dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi, da ya zo na uku ya samu kuri’u miliyan shida da dubu dari da daya da dari biyar da talatin da uku (6,101,533).
Shi kuwa dan takarar jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso da ya zo na hudu, ya samu kuri’a miliyan daya da dubu dari hudu da casa’in da shida da dari shida da tamanin da bakwai (1,496,687).
0 Comments